Koriya ta Kudu ta ba da rahoton harbuwar karin mutum 2,109 da sabon nau’in cutar COVID-19 a cikin makon jiya, wanda ya kawo jimlar masu ita a kasar zuwa 8,125.
Ma’aiaktar Lafiyar kasar ta sanar a ranar Talata cewa daga cikin sabbin wandada aka gano daga ranar 25 ga Yuli, mutum 240 baki ne daga kasashen waje, sauran mutum 1,869 kuma sun harbu ne a cikin gida.
- Rikicin Filato ya lakume rayuka 17 da gine-gine 85 —’Yan sanda
- ‘Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Alhakin Al’umma Ne’
Ta ce cabbin mutum 1,929 da suka harbu sun fito ne daga wurare daban-daban daga cikin kasar.
A cewar Hukumar Kula da Cututtuka ta Koriya (KDCA), ta bayyana cewa yawaitar mutanen da suka harbu da cutar a cikin kasar ya nuna yadda take dada tasiri.
A halin da ake ciki, kasar ta tabbatar da samun Karin mutum biyu da suka kamu da samfurin COVID-19 na Delta.
Koriya ta Kudu ta ba da rahoton samun karin mutum 1,202 da COVID-19 ta harba cikin awa 24, wanda ya kawo adadin masu cutar zuwa 202,203 a kasar.
Yawan wadanda ke kamuwa da cutar a mako na haura mutum 1,000.