Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya ce gwamnatinsa ta kubutar da mutum 2,000 daga hannun ’yan bindiga ta hanyar yin sulhu.
A cewarsa, sama da ’yan bindiga 62 ne suka ajiye makamansu tare da tuba tun bayan zuwan gwamnatinsa.
- Mohamed Bazoum: Wane ne sabon Shugaban Nijar?
- ‘Ni na koya wa Ali Nuhu da Adam Zango rawa’
- An ceto mai gari da wasu 3 da aka yi garkuwa da su
- Kwastam ta kama tabar wiwi na biliyan N1 a Legas
“’Yan bindigar da suka tuba da kansu suke taimaka mana wajen wajen bayyana shugabannin ’yan bindiga da sansanoninsu don tattaunawa da yin sulhu. Tun da aka fara sulhu sai da aka yi wata takwas a Zamfara ba tare da an kai hari ba, sai kwana-kwanan nan,” cewarsa.
Wannan kalamai na Matawalle sun fito je ta bakin Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Ibrahim Magaji Dosera, a ranar Juma’a, inda ya ce wanda suka tuban suna taimaka wa Gwamnatin Jihar yadda ya kamata.
Sai dai gwamnan ya koka kan rashin samun isashshen gudunmawa daga Gwamnatin Tarayya, da kuma karancin jami’an tsaro da za su yaki ta’addanci a yankin Arewa maso Yammancin Najeriya.
“Yanzu ku amsa min, wanne ne ya fi ga gwamna? Ya nade hannunsa ana kashe mutane ko kuma ya yi sulhu da ’yan bindiga don samun masalaha, wanne ya fi?” inji shi.
Ya kara da cewa, tunda ya karbi mulki, ake gudanar da tarukan masu ruwa da tsaki na jihar da suka hada da; ’yan Majalisa, malaman addini, shugabannin al’umma, masu sarautun gargajiya, shugabannin Fulani da sauransu, don nemo mafita daga halin da jihar ke ciki.
Taron da ake gudanarwa karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, na haifar da kyakkyawan sakamako, inji gwamna Matawalle.
Sai dai ya ce hare-haren da aka kai baya-bayan nan sun samo asali ne daga yadda wasu suke daukar nauyin aikata ta’addanci kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.