✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 20 sun mutu a ruwa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja

An tafka asarar rayuka a kogin Guni-Zumba sakamakon harin da ’yan bindigar suka kai kauyukan Guni da Kurgbaku.

Akalla mutum ashirin ne suka rasa rayukansu ciki har da mata da kananan yara, sakamakon nutsewar da suka yi a kogi a yayin da suke kokarin tsere wa farmakin ’yan bindiga a Jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa an tafka asarar rayukan ne a kogin Guni-Zumba biyo bayan harin da ’yan bindigar suka kai kauyukan Guni da Kurgbaku da ke Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun kai hare-haren ne da safiyar ranar Laraba, lamarin da ya sanya mazaunan kauyukan Kurgbaku da Guni suka tsere.

Wasu majiyoyi da Aminiya ta ruwaito daga garesu sun shaida cewa wadanda lamarin ya rutsa da su sun nutse a ruwan a sakamakon cika makil da suka yi a wani kwale-kwale a kokarinsu na ketare wa kogin Guni-Zumba zuwa wani sansanin ’yan gudun hijira domin samun mafaka.

Wani mazaunin yankin mai suna Shehu Abubakar, ya shaida wa wakilinmu cewa an yi kwale-kwalen lodi da jama’a fiye da kima, lamarin da ya kai ga kifewarsa a tsakiyar ruwa.

Neja da ke yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya na daga cikin yankunan Arewacin kasar da suka hada da Zamfara, Sakkwato, da Kaduna da kuma Katsina, da ke fama da hare-haren ’yan bindiga, wadanda gwamnati ta ayyana su a matsayin ’yan ta’adda.

Ko a farkon watan nan na Maris sai da gungun ’yan bindiga suka sace wata Amarya da wasu daga cikin masu yi mata rakiya zuwa gidan mijinta, yayin da suke kan hanyarsu daga kauyen Allawa na Karamar Hukumar Shiroro zuwa garin Fandogari na Karamar Hukumar Rafi a Jihar.