Akalla mutum 20 sun kamu da cutar kuturta a Jihar Kogi bayan da aka yi ikirarin cewa babu cutar a jihar.
Jami’ar Shirin Yaki da Cutar Kuturta ta Kasa (NLM) a Jihar Kogi, Hannah Fashona ce ta bayyana haka a taron raba kayan tallafin COVID-19 ga masu cutar da sauran nakasassu a Lokoja.
- An yi garkuwa da dalibai 8 na Jami’ar Ahmadu Bello
- Buhari ya shiga ganawar sirri da Majalisar Tsaro ta Kasa
- An rataye mutum 21 saboda aikata ta’addanci
Hannah Fashona ta bayyana cewa an sake samun mutanen da suka kamu da cutar ne a tsakanin watan January zuwa Nuwamba, 2020.
Ta ce kungiyar na kokarin kawar da cutar daga Nijeriya, kuma cibiyarta da ke Ochadamu a jihar ta yi nasarar kula da wasu masu cutar.
A cewarta, tsoro da jahilci sun sa sama da mutum miliyan uku a duniya na rayuwa da kuturtar da ba a gano ba wanda kuma ke illa ga lafiyarsu.
Ta kara da cewa sama da mutum 600 ne ke kamuwa da cutar a duniya a kullum kuma fiye da rabinsu yara ne.
Hakan ce a cewarta ta sa suke ci gaba da bincike domin ganin an kawar da cutar gaba daya a fadin duniya.
Amma duk da haka ta nuna rashin jin dadin bayanin Gwamnatin Tarayya cewa Najeriya ba ta cimma nasarar kawar da cutar ba.
“Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya a kwanan nan ta ce ta dauki matakin yaki da cutar, amma ana kara samun masu kamu da ita”, inji ta.
A cewarta wasu daga cikin marasa lafiyar ba sa zuwa da wuri sai baya cutar ta kai mataki na daya ko na biyu wanda ke da wuyar magani.
“Sai sun gama zuwa wurin masu maganin gargajiya kafin su zo cibiyar da ke Ochadamu samun mafita; Dole Gwamnatin Tarayya ta shigo a kawar da cutar”, inji ta.