Ana fargabar mutum biyu sun mutu wasu sama da 37 sun samu ranuni sakamakon rushewar wani bene a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
An garzaya asibiti da mutun 37 da aka ciro daga baraguzan ginin da ya rushe a unguwar Garki Village da ke Abuja.
- Sunayen unguwannin da Wike zai yi rusau a Abuja
- Jami’in DSS ya soka wa tsoho wuka kan N3,000
- Ministan Abuja ya haramta tallace-tallace
Ikharo Atttahh, Hadimin tsohon ministan Abuja, Mohammed Bello ya tabbatar da alkaluman mamatan da wadanda suka samu rauni, inda ya wallafa bidiyon al’a,amarin.
A halin yanzu masu aikin ceto na kokarin ciro ragowar mutanen da suka makale a cikin baraguzan ginin da ibtila’in ya auka masa a cikin daren Laraba.
Wani mazaunin yankin Garki ya tabbatar mana da faruwar lamarin amma bai yi karin bayani ba.
Kawo yanzu dai hukumomi ba su ce komai game da lamarin, wanda shi ne rushewar gini na farko, kwana biyu bayan fara aikin sabon minista, Nyesom Wike.
Za a iya tunawa a jawabin Wike na karbar rantsuwa ya yi alkawarin rushe duk gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a birnin.