Zanga-zangar #EndSARS a yankin Apo dake Babban Birnin Tarayya Abuja ya rutsa da wasu matasa 2 a ranar Litinin.
Matasan wadanda ke sana’ar acaba sun gamu da ajalinsu ne bayan masu zanga-zangar sun auka masu a yankin.
Matasan, a cewar rahotanni, sun samu kansu ne a yankin na APO ta inda masu zanga-zangar su ka fito.
Tun da farko dai masu zanga-zangar ta #EndSARS sun yi yunkurin kutsawa wani gareji a yankin inda masu sana’ar babura mai masu kafa uku ke yada zango, sai kuma masu motocin tasi a daura da su.
Wani da lamarin ya rutsa da shi a wajen, ya shaidawa Aminiya cewa wadanda ke wajen sun nemi hana masu zanga-zangar kaiwa ga wajen, lura da irin makaman da wasu daga cikinsu ke rike da shi, inji shi.
“Sai dai daga bisani sun kutsa wajen sannan suka kona wasu motoci da kayan tireda, a yayin da wadanda ke wajen su ka ja baya ganin lamarin ya fi karfinsu,” inji shi.
Kazalika, wata majiya ta ce daga baya matasan da a ka yi wa barnar sun sake komawa cikin shiri, sannan su ka ketara ta bangaren masu zanga-zangar inda su ma su ka kona masu kayan sana’a na gefen titi, inji majiyar.
Hakan a cewarsa yasa yanzu kowa ya ja daga, kowa ya kiyayi shiga bangaren wani.
Ana cikin hakan ne sai a ka sami labarin kashe ‘yan acaban biyu a daya bangaren tare da kona baburansu biyu.
Daga bisani dai an ga ayarin ‘yan sanda tare da jami’an tsaro na NSCDC na kutsawa ta yankin da nufin kwantar da kura.