✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 2 sun gurfana a gaban kotu kan zargin bata sunan Ganduje a wasan barkwanci

A bidiyon barkwancin, sun nuna Ganduje ba ya ganin fili ya kyale bai sayar ba

A ranar Laraba aka gurfanar da wasu mutum biyu a Kotun Majistare da ke Nomansland a Kano, kan zargin bata sunan Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Bayanan farko sun nuna wadanda ake zargin sun wallafa wani bidiyon barkwanci a dandalin Facebook inda a ciki suka ce Gwamnan ba ya ganin fili ya kyale, kuma wai ya cika barci sosai.

Bayan karanta bayanan farko, wadanda ake kara sun amsa tuhumar da ake yi musu.

Lauyan mai gabatar da kara Barista Wada Ahmad Wada, wanda babban lauya ne a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, ya nemi a yi masa shari’a a kan mutane biyun da ake kara.

Kotun ta sami mutanen da ake zargin da aikata laifin, ta kuma dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar bakwai ga watan Nuwamba don yanke hukunci.