✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 17,000 cikin wata 5 a Amurka – Bincike

Mahara da 'yan dadi bindiga na kasashe mutane kullum a Amurka.

Akalla mutum 17,000 ciki har da kananan yara 650 mahara suka kashe cikin watanni biyar, kamar yadda wasu alkaluma da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya fitar suka nuna.

Alkaluman da AFP ya tattara sun nuna cewa ana kashe mutum 111 a kowace rana a fadin Amurka, wanda ya mayar da jumullar mutanen da ke rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren ’yan bindigan zuwa dubu 41 a kowace shekara.

A cewar kungiyar Everytown, zuwa yanzu makamantan hare-haren ‘yan bindiga dadi ya karade ko ina a sassan Amurka, inda a jihar Texas da ke da kwarya-kwaryar dokar sayar da makamai ke da mutum akalla 3,600 da ke mutuwa a sanadin harin ‘yan bindiga dadi.

A wannan shekara akalla mutum 17,199 hare-haren ‘yan bindigar ya yi sanadin mutuwarsu ciki har da dalibai yara 19 da malamansu biyu da wani dan bindiga ya harbe a wata makarantar firamare da ke jihar Texas a ranar laraba.

A 2021 kuwa, mutum 45,000 ne suka mutu a hare-haren ’yan bindiga a Amurka.

Har wa yau, an yi wa mutum 20,920 kisan-gilla wanda shi ne mafi muni tun bayan 2017, lokacin da aka kashe mutum 58,000 a sanadin ire-iren wadannan hare-hare.

Alkaluman sun kuma nuna yadda a cikin wata biyar mutum 14,000 da suka samu munanan raunuka a sanadiyyar harin ’yan bindigar, wanda galibi ke da nasaba da nuna wariyar launin fata.