Hukumomin kasar Bangladesh sun ce zuwa ranar Asabar rayukan mutane 16 ne suka salwanta bayan da wani abin fashewa ya janyo gobara a wani masallaci da ke Dhaka, babban birnin kasar.
Fashewar ta auku ne da yammacin ranar Juma’a yayin da Musulmi ke gudanar da Sallar Maghriba a masallacin Baitus Salat Jame da ke gundumar Narayanganj mai tazarar kilomita 25 daga kudancin Dhaka.
Masu bincike sun ce alamu na nuna cewa wata na’urar sanyaya daki ce ta yi tartsatsin da ya haddasa gobarar lokacin da ta fara aiki bayan dawo da wutar lantarki, saboda samuwar iskar gas a wurin.
- Mali: Sojoji Sun Dage Taron Kafa Gwamnatin Farar Hula
- Jerin Kasashe Da Saudiyya Ta Gindaya Wa Sharadin Shiga Cikinta
Shugaban Hukumar Kwana-kwana ta Narayanganj, Abdullah Al Arefin, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa iskar gas din ce ta shiga masallacin.
“Da suka rufe tagogi da kofofin masallacin sannan suka kunna na’urar sanyaya daki, sai aka samu tartsatsin lantarki wanda ya haddasa fashewar”, inji shi
Wani jami’in rundunar ’yan sanda, Zayedul Alam, ya ce an yi gaggawar garzayawa da mutum 37 cikin 40 da suka yi munanan raunuka zuwa wani asibitin kwararru da ke birnin Dhaka.
Sai dai kafin wayerwar gari mutum goma sun riga mu gidan gaskiya a asibitin kamar yadda wani kwararren likita, Partha Sankar Paul, ya zayyana wa manema labarai.
“Wani yaro mai shekeru bakwai wanda kusan duk jikansa wuta ta kone ya ce ga garinku nan sa’o’i kadan bayan kwantar da shi”.
Hotunann bidiyon da gidajen talabijin suka yada sun nuna yadda ’yan uwan wadanda ajalin ya katse wa hanzari ke jimami a wajen asibiti.