✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno

Mayaƙan sun gindaya sharaɗin sako ragowar mutanen uku da ke hannunsu.

Aƙalla mutum 11 sun shaƙi iskar ’yanci bayan kuɓuta daga hannun ƙungiyar mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi a Jihar Borno.

Waɗanda suka shaƙi iskar ’yancin na daga cikin mutanen da ƙungiyar Boko Haram ta sace a wani wurin kamun kifi a Doron Baga.

Wata majiya ta bayyana cewa, wani kwamandan ’yan ta’addan mai suna Tar ne ya jagoranci garkuwa da mutanen ne a ranar 13 ga watan Fabrairu 2025.

Tar da tawagarsa da ke addabar masunta da manoma a gaɓar Tafkin Chadi sun ɗauke mutanen ne yayin da suka afka wa al’ummar Shawaram da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Kukawa ta jihar, inda suka yi awon gaba da mutane 14 da suka haɗa da mata da ƙananan yara.

Wani shugaban al’ummar yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun nemi kuɗin fansa jim kaɗan bayan sace su.

Ya bayyana cewa an ceto mutane 11 bayan an biya kuɗin fansa na Naira miliyan 1.4 da wasu al’umma suka tara.

A cewarsa, har yanzu akwai mutane uku da ake garkuwa da su —ciki har da mace guda mahaifinta — a hannun ’yan ta’addan.

Majiyar ta ce mace ta zaɓi ci gaba da zama a hannun ’yan ta’addan saboda sun ƙi sakin mahaifin nata.

Majiyar ta ƙara da cewa Tar ya gindaya sharaɗin cewa muddin ba a biya musu buƙatar sako ragowar mutanen uku ba, zai aurar da macen da ke cikinsu tare da ɗaukar hukunci mai tsanani kan sauran waɗanda ke hannunsa.

Sai dai har zuwa yanzu mahukuntan da wakilinmu ya tuntuɓa ba su ce komai dangane da lamarin ba.