✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 11 sun kone kurmus a hadarin mota a hanyar Legas

Hadarin wanda ya rutsa da mutum 18, an ceto bakwai daga ciki, amma 11 su kone kurmus.

Mutum akalla 11 ne suka kone kurmus sakamakon wani hadarin mota da ya rusta da su a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a Jihar Oyo.

Mai magana da yauwn hukumar kiyaye hadura ta kasa ta shiyyar Ogun, Florence Okpe ce ta tabbatar da hakan a ranar Lahadi.

Ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 10:20 na dare a ranar Asabar a kusa da Gadar Isara, inda hatsarin ya rutsa da mutum 18.

Okpe ta kara da cewa gudun wuce kima da kuma karya ka’idojin tuki ne suka haddasa hatsarin da ya jawo mutuwar mutanen.

A cewarta, hadarin wanda ya rutsa da mutum 18, an ceto bakwai daga ciki, amma 11 su kone kurmus ta yadda ba a iya ko gane su.

“An kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Victory da ke Ogere amma mahukuntansa sun ki karbar daya daga cikinsu, amma daga karshe an garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Babcock da ke Ilisan”

Karo da motocin suka yi ya haifar da fashewa da tashin gobara, inda ya kunshi motoci uku, a cewar Okpe.