Hukumar gudanarwa ta ‘yan sandan Najeriya PSC ta ce ta samu takardun mutum dubu 104,289 da suka cike shafin neman aikin hukumar.
Kakakin hukumar ‘yan sandan Najeriya PSC Ikechukwu Ani, ne ya sanar da hakan inda ya ce, yau kwana 12 da bude shafin intanet don neman aikin ‘yan sandan da ake da bukatar cike gurbi na dubu 10, amma adadin ya wuce gurbin da ake so.