Wani hari da ’yan bindiga suka kai kan jami’an tsaro a Arewacin kasar Mexico ya yi sanadin mutuwar mutum 10 a ranar Litinin.
Sakataren Tsaron Jama’a na yankin Nuevo Leon Gerardo Palacios ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa “Wasu mutane da ke tafiya a cikin manyan motoci uku masu sulke sun kai hari da bindigogi.”
- Muna bin gwamnati bashin tiriliyan 2.8 na tallafin man fetur – NNPC
- Gwamnan Sakkwato ya soke duk mukaman da Tambuwal ya bayar tun daga watan Maris
Ya kara da cewa an kashe akalla mutum 10 da ake zargi da aikata laifuka tare da jikkata jami’ai hudu.
An kai harin ne a kan wata babbar hanyar da ke tsakanin jihohin Nuevo Leon da Tamaulipas a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da manyan laifuka.
Hanyoyin da ke tsakanin jihohin biyu sun kasance wuraren da ake yin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.
An kashe mutane sama da 340,000 a kasar Mexico, an kuma samu bacewar wasu 100,000 — wadanda aka danganta su ga kungiyoyin masu aikata laifuka — tun bayan da gwamnatin kasar ta kaddamar da yaki da miyagun kwayoyi a 2006.