Mutanen kauyuka da dama a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya suna hada kudi suna sayen bindigogi da sauran makamai domin kare kawunansu daga ’yan bindiga da ’yan ta’adda da sauran miyagu.
Aminiya ta gano daidaikun masu kudi ma suna sayen bindigogi domin kare kawunansu daga masu auka musu ko su saya su ba wasu kungiyoyin jama’a.
- Abin Da Ya Sa Tashe-Tashen Hankula Suka Ki Karewa A Najeriya
- Yadda ’yan bindiga suka sako Daliban Islamiyyar Tegina
Mutanen kauyuka a jihohin Neja da Zamfara da Kaduna da Filato da Katsina ne a kan gaba wajen sayen makaman da suka hada da bidigogi domin kare kansu saboda yadda suke fama da matsalar tsaro shekara da shekaru.
Kusan kullum sai an ambaci jihohin a ’yan shekarun nan, saboda akasarin labaran da suke fitowa daga gare su na kashe-kashe da barnata dukiya ce da miyagu daban-daban suke aikatawa.
Kuma a yayin da mazauna yankunan ba sa iya zuwa gonaki don yin noma ko kuma kasuwanni, saboda tsoron kai musu farmaki, wadansu ma ba sa iya kwana a gidajensu.
Shugabannin al’umma da mazauna yankunan da suka tattauna da wakilanmu, sun ce sun yanke shawarar komawa ga kare kawunansu ne, saboda ba a tura jami’an tsaro su kare su, ko kuma ’yan kalilan da ake turawa aikin ya fi karfinsu.
Aminiya ta gano cewa shugabannin al’umma suna kara tabbatar da matsayin gwamnoninsu ne wadanda a lokuta da dama suke nuna damuwa da munin rashin tsaro a yankunansu.
A matsayinsu na manyan jami’an tsaro a jihohinsu, gwamnoni da dama sun sha fadin cewa matsalar tsaron ta fi karfinsu, duk da cewa a wasu lokuta sukan “tsara” ayyukan ’yan banga ko ’yan sa-kai da maharba don karfafa tsaron.
Misali Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum a lokuta da dama ya sha fadin cewa ’yan banga sun taimaka wajen magance matsalolin tsaro a jiharsa.
A lokacin da yake karbar lambar yabo a Owerri a watan Mayun bana, ya ce, “Mu a Jihar Borno muna fama da matsalolin tsaro sama da shekara 12, sai dai ana ta gudanar da sauye-sauye, kuma daga cikin abin da muke yi, don inganta tsaro a jihar akwai tsoma ’yan banga; sun karbi aikin sanya ido kan tsaro a jihar ta yadda suka kora ’yan ta’adda zuwa dajin Sambisa daga jihar.”
Aminiya ta gano cewa, a yayin da wasu kauyuka suke sayen bindigogin harba-ka-ruga, wasu suna sayen bindigogin zamani ne da suka hada da fistol da ribalba da masu bakuna biyu a wasu lokuta da samfurin AK-47.
Da dama daga cikin wadanda suka tattauna da wakilanmu kan batun sun ce baya ga cim-ma matsaya a tsakanin mutanen kauyukan, a wasu kalilan lokuta sukan nemi lasisi daga hukumomin da suka kamata kafin su sayi bindigogin.
– Jihar Neja
Wata majiya a wani kauye da suka sha wahala daga hare-hare a Karamar Hukumar Shiroro ta shaida wa Aminiya cewa, duk da ba su iya mallakar manyan bindigogi da ’yan bindigar suke amfani da su, su ma sun koma ga kare kawunansu ta hanyar amfani da bindigogin da ake kerarwa a gida.
“A kwanakin bayan nan mun kashe ’yan bindiga kusan 10, lokacin da suka kawo mana hari,” inji majiyar.
Sai dai wata majiya a wani kauye Karamar Hukumar Rafi da suka yi fama da hare-haren, ta ce su ba su goyon bayan jama’a su sayi bindigogin.
“An kawo shawarar mu sayi bindigogin, amma mutanen kauyenmu ba su goyi bayan haka ba, saboda idan hakan ya magance matsalar a yanzu, zai iya jawo wata matsalar a nan gaba. Idan mutane suka samu matsala a nan gaba za su iya amfani da bindigogi a kan junansu,” inji majiyar.
Kokarin jin ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane don ya yi magana kan lamarin ya ci tura har zuwa hada wannan rahoto.
Mazauna kauyukan Kaduna da Filato suna samar wa kansu bindigogi
A shekara uku da suka gabata, wasu kauyukan da suke fama da matsalar tsaro a Jihar Kaduna sun rika sayen bindigogi domin kare kawunansu daga ’yan bindiga.
Wakilanmu sun ce kauyuka a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Igabi da Chikun, sun bayyana yadda a yanzu suke sanya matasa su rika gadin kauyukansu daga farmakin ’yan bindiga.
Wani mutumin Karamar Hukumar Giwa ya shaida wa Aminiya cewa: “Mun dade da sanin cewa gwmanati ba za ta iya kare mu ba, don haka yanzu muke kare kawunanmu, kuma ba mu bukatar wata amincewa daga wani don yin haka.”
Wani mutumin kauyen Igabi ya shaida wa Aminiya cewa, idan suna kare kuayukansu ta hanyar fafata harbe-harbe da ’yan bindigar sai ’yan bindigar su koma kauyukan da ba su da bindigogin da za su kare kawunansu.
“Mun lura babu dalilin gudu daga gidajenmu saboda za su sake dawowa. Don haka ya fi dacewa mu tsaya mu kare gidajenmu koda za mu rasa rayukanmu,” inji majiyar.
Aminiya ta gano haka lamarin yake a wasu kauyukan Jihar Filato, inda makera suke kera bindigogi ga mutanensu don kare kawunansu daga hare-hare.
“Wadansu daga cikinmu sun samu lasisi daga hukumomi inda suka sayi bindigogi,” inji wani dan kasuwa da ba ya son a bayyana sunansa.
Ya kara da cewa: “Hatta AK-47 ba ta da wahalar saya a yanzu, saboda wadansu mutane suna shigo da su ga wanda zai iya saye. Wannan ce kawai hanyar da za ka kare kanka da iyalanka da dukiyarka,” inji shi.
– Jihar Zamfara
Mazauna kauyuka da dama a kananan hukumomin Jihar Zamfara 14 ma suna tara bindigogi domin kare kawunansu daga ’yan bindigar.
Bincike a kauyukan ya gano cewa mutanen kauyukan tuni sun daina tunanin dogara da jami’an hukumomin tsaro na gwamnati don su kare su.
Misali a wata masarauta, akwai kauyukan da aka sani da jarumta idan aka zo batun kare kawunansu ta yadda miyagu masu dauke da bindigogi suke tafka hasara a duk lokacin da suka kai farmaki ga kauyukan.
“Muna sayen makamai… kowane gida ko kowane mutum yana da bindiga, kuma idan muka hango matsala tana zuwa mukan fito gaba daya mu kare kawunanmu, kuma wannan yana taimaka mana,” inji wani shugaban al’umma wanda ba ya son a fadi sunansa saboda dalilan tsaro.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa: “Akwai lokacin da suka kawo mana hari a nan kauyen. Mun yi musu muguwar barna, mun tilasta sun gudu ba shiri bayan mun samu nasara a kansu.”
Wailinmu ya samu bayanin cewa a wasu hedkwatocin kananan hukumomi da manyan garuruwa ana samun masu dukiya suna sayen bindigogi ga ’Yan Sa-kai.
“Masu dukiya suna tallafa wa ’Yan Sa-kai wajen saya musu bindigogi kirar gida da tocila da adduna da masu da sauransu,” inji shi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa mazauna jihar a baya sun kafa tare da samar da makamai ga kungiyoyin ’yan banga ko ’Yan Sa-kai amma hukumomi a jihar suka hana su daukar makamai a lokacin sulhun baya da ’yan bindiga wanda ya ruguje.
Daga baya da suka fahimci ’yan bindigar ba da gaske suke yi ba, wajen mika makamansu, kungiyoyin sa-kan sun sake sayen makamai inda suka sha alwashin ba za su sake mika wuya ga miyagun ba.
– Jihar Katsina
A Katsina, wadansu mutanen jihar sun shaida wa wakilinmu cewa duk da cewa kiran da Gwamna ya yi na jama’a su tanadi makamai don kare kansu abu ne mai karfafa zuciya.
Sun ce sai dai an riga an makara, lura da galibin kauyukan da ’yan bindigar suka rika kai wa hari ba su da halin sayen bindigogin.
Wani mazaunin Batsari, garin da aka kai wa hari a baya-bayan nan ya ce, “Ko ma za mu sayi bindigogin ba za mu iya sayen wadanda za su kai na ’yan bindigar ba. Wasu daga cikin makaman da suke da su, ba mu taba ganinsu ba ko a hannun jami’an tsaro.”
Shi ma Salisu Sani (ba sunansa na gaskiya ba ne) mazaunin Kurfi ya ce wadansu masu hannu da shuni sun sayi manyan bindigogi don kare kawunansu ko da za a kai musu hari.
“Ni dan kwamitin tsaro ne na yankinmu, na san abubuwa da dama da suke gudana.
“Ina tabbatar maka lamarin kamar na sauran kananan hukumomin da abin ya shafa ne kamar Batsari da Safana da Danmusa da Jibiya, saboda muna aiki tare ta hanyar bayar da bayanan sirri.
“Kuma na san wadanda suke da lasisin mallakar bindiga don kare kansu,” inji shi.
– Lauyoyi sun soki mallakar bindigogi ba bisa doka ba
Lauyoyi sun yi gargadin cewa duk da doka ta amince da kare kai, sun ce amfani da bindigogi ba bisa doka ba yana iya cutar da jama’a a nan gaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan kiraye-kirayen da wadansu gwamnonin jihohi suke yi na a kyale mutane su mallaki bindigogi don kare kawunansu, wani babban lauya, Farfesa Paul Ananaba (SAN) ya ce shawarar muguwar shawara ce da za ta iya illa ga al’umma a nan gaba.
Don haka ya shawarci gwamnonin jihohin cewa maimakon haka su tallafa wa hukumomin tsaro.
“Idan lamarin ya damu gwamnonin, ba daidai ba ne su ce kowa ya mallaki bindiga kuma su kare kansu saboda ’yan bindiga, wadanda suke da miyagun bindigogi da za su iya jawo karuwar hasarar rayuka.
“To mene ne amfanin shugabancin ke nan? Suna iya neman Gwamnatin Tarayya ta kafa dokar ta-baci,” inji shi.
– Kafa ’yan sandan jihohi
Shi kuwa Dayo Akinlaja (SAN) kira ya yi a amince da ’yan sandan jihohi kamar yadda wasu jihohi suke ta nema.
“Amma a gaskiya ba zai yi kyau ga daukacin al’umma ba, domin ba kowa ne zai iya rike amanar kula da bindiga ba,” inji shi.
Akwai masu ra’ayin cewa in ma za a bar mutane su mallaki bindigogin to wajibi ne a samar da irin bindigogin da miyagun suke amfani da su ba kananan bindigogi ba.
Miyagun bindigogi dai suna shigowa kasar nan ne ta iyakoki da tashoshin jiragen ruwan kasar nan.
“Misali a shekarar 2017, an kama wani jirgin ruwa dauke da bindigogi 440 a Legas, bayan an ce farin siminti ne aka sayo.
– Kwastam ta kama bindigogi 4,000
Gaba daya ma’aikatan Kwastam sun kama bindigogi kusan 4,000 a lokuta daban-daban a shiyyarsu ta Neja da Kwara da Kogi.“
A Janairun 2018, Kwastam sun kama wani sunduki dauke da akwatuna 49 makare da bindigogi 661.
Bindigogin da aka dauko su a wata babbar mota kirar Mack, an kama ta a Titin Mil 2 Titin Apapa, Legas.
Wata kididdiga da Aminiya ta yi ta gano a bara kadai an kama akalla mutum 4,338 a sassan kasar nan, inda aka kama bindigogi 255 da harsasai 2,204.
Sannan an kama kusan harsasai 1,417 ciki har da nakiyoyi uku daga wandada ake zargi.
Rahotanni daga Lami Sadiq, Kaduna da Shehu Umar, Gusau da Tijjani Ibrahim, Katsina da Abubakar Akote, Minna da Fidelis Mac-Leva da John C. Azu da Idowu Isamotu da Faruk Shu’aibu, Abuja.