✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda mutanen gari suka kama ’yan bindiga a Zariya

Mutanen gari sun yi kukan kura sun kama masu garkuwa da mutane a Zariya.

Mutanen gari sun yi kukan kura sun cafke masu garkuwa da mutane da suka kai hari a unguwar Low Cost da ke Zariya.

A halin yanzu, wasu daga cikin ’yan bindigar suna hannun ’yan sanda bayan da mutanen unguwar suka yi musu kofar rago ranar Lahadi da tsakar dare.

Duk da haka, masu garkuwar sun tafi da matan aure biyu daga gidaje daban-daban, amma sun sako kananan yara biyun da suka dauka da tare da daya daga cikin matan, sai dai ba su sako mahaifiyar yaran ba.

Majiyarmu a Zariya ta ce ’yan bindigar sun harbi kananan yara almajirai guda hudu a lokacin farmakin da suka kai.

Aminiya ta gana da almajiran da raunukan harin a jikinsu, kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibitin New City da ke a Zariyan.

Karin bayani na tafe.