Aƙalla mutum 213 ne suka rasu a sakamakon turereniya a sassan Najeriya a shekaru 11 da suka ta gabata.
Mafi yawan turereniyar da suka yi ajalin mutanen sun faru ne a wurin rabon tallafin abinci. Wasu kuma na da nasaba da jarabawar ɗaukar aiki sai kuma tarukan addini.
A cikin kwanaki shida da suka gabata turmutsutsi a wurin rabon tallafin abinci ya yi ajalin mutane 72 a jihohin Oyo, Anambra da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Aƙalla ƙananan yara 40 ne aka tabbatar da rasuwarsu a wurin taron bikin yara da tsohuwar matar Ooni na Ife, Naomi Shikemi, ta shirya ranar Laraba, a makarantar Islamic High School da ke yankin Bashorun na birnin Ibadan a Jihar Oyo.
A ranar Asabar kuma wasu yara 32 suk rasu a turmutsutsin da aka samu a Abuja da jihar Anambra. Yara 10 ne suma rasu a Abuja, sai wasu 22 a Anambra, wasu da dama kuma suka ji raunuka.
Misis Oniyide, mahaifiyar daya daga cikin yaran da suka rasu a turmutsutsin Ibadan, ta ce, “ban san za a yi rabon abinci ba, babu wanda ya gaya min, ’yata Aina mai shekara 10 ba ta gata min ba. Da safe ta fita tallar akamu yadda ta saba, sai da tsakar dare muka gano gawarta a wani asibiti.”
Wani jami’in gwamnati mai suna Michael Obi, ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan ɗan uwansa “ta fbar gida da safe tare da wasu yara, amma ba ta dawo ba. Da muka samu labarin turmutsutsin ba mai damu ba, mun ɗauka abin da sauƙi, ba mu sani ba, ashe ajalinta na cann. Haka Allah Ya so.”
Ya ce suna shirin tura yarinyar gida ƙauye domin yin Kirsimeti tare da iyayenta, amma suka ce bari su jira a kammala bikin rabon shinkafa na shekara shekara na Obiejesi.
Ita kuwa, Misis Margaret Edozie, wadda ɗanta ya rasu cewa ta yi: “Yaya uwa za yi a ce a irin wannan lokaci za a binne ɗan cikinta? Bana Kirsimeti ta zo mana cikin baƙin ciki.”
Wani ganau, Peter Uche, ya ce, “da mutane sun nutsu sun bi tsari cikin kwanciyar hankali, da babu abin da zai jawo rige-rige da turmutsutsin. Akwai shinkafar da za ta ishi kowa a wurin.
“Amma wasu mutanen maimakon su ɗauki buhu daya, sai suka riƙa ɗiba da yawa, a garin haka ne tsautsayin ya ritsa da masu raunin cikins. Abin takaici.”
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a turmutsutsin Abuja ya ce, da misalin ƙarfe 4.30 na asuba na zo nan karɓar shinkafa, amma wasu mutane maimakon su bi layi, sai suka riƙa turereniya, hakan ya haifar da yamutsi, dole na koma gefe da na lura abin ya wuce gona da iri.”
Wani likita a Asibitin Maitama a da ke Abuja inda aka kai waɗanda suka ji rauni ya ce an sallami mutum shida ranar Asabar, saura wasu biyu da ake jinyar su, “amma muna fatan sallamar su zuwa ranar Litinin.”
Mace-mace a wurin turereniya
Tariyar da a muka gudanar ta nuna mutum 213 ne suka rasu a wurin turereniya a shekara 11 da suka gabata a Najeriya.
A shekarar 2024 kaɗai an samu turereniya sau bakwai a wurin rabon abinci, inda mutane 96 suka rasu.
Kafin guda uku da aka samu a makon jiya a Ibadan da Anambra da Abuja, a watan Fabrairu an samu turereniya a yankin Yana a Jihar Legas, a cibiyar da hukumar kwastam ta ware domin sayar da shinkafar da kwace a kan N10,000 kowane buhu.
A watan Maris mutu bakwai suka rasu a wurin rabon Zakka, wanda kamfanin Shafa Holdings ya gudanar a garin Jos a Jihar Filato.
A watan Afrilu kuma wasu mutum tara suka rasu, wasu 30 suka ji rauni a turereniyar rabon tallafin abinci da Sanata Aliyu Magatakarda Wamako ya gudanar a yankin Gawon Nama da ke garin Sakkwato.
A watan Maris kuma dalibai mata biyu suka rasu a turereniyar da ta auku a filin taron yaye dalibai a Jami’ar Jihar Nasarawa.
A watan ne akalla matasa 16 suka rasu a wurin jarabawar ɗaukar aikin hukumar shige da fice a birnin Abuja da Muna da Fatakwal da kuma Benin.
A ranar 2 ga watan Nuwamba muka mutane 25 suka rasu, wasu 200 suka jikkata a taron ibada a cocin Holy Ghost Adoration da ke yankin Uke, Karamar Hukumar Idemili ta Kudu a Jihar Anambra.
Ranar 16 ga Oktoba 2013, an samu turereniya da ta yi ajalin mutum 20 da jikkata wasu da dama a wurin rabon tallafin abincin Karamar Sallah da Sanata Bukola Saraki ya gudanar a garin Ilorin, Jihar Kwara.
A watan Agustan 2022 mutum suka rasu a Legas a wurin taron ibadar Cocin Comfort Life Mission International da ke yankin Ikotun.
Ranar 28 ga watan Mayun 2022, an tabbatar da mutuwar mutane 31 da jikkatar wasu da dama a wurin rabon abinci a Fatakwal, Jihar Ribas, wanda cocin King’s Assembly ya gudanar.
A watan Fabrairu 2020, mutum 23 sun rasu a lokacin da gwmanatin jihar Borno ke rabon tallafin abinci ga ’yan Najeriya da ke gudun hijira a Nijar.
Mataimakin shugaban kasa Kashin Shettima ya bayyana takaici bisa mace-mace da suka auku wurin rabon tallafin abinci, yana mai alkawarin tallafa wa iyalan mamatan.
Ministan yada labarai a nasa sakon ya da umarnin yin kyakkyawan tsari kula da cunkoso a duk lokacin za a yi rabon kayan tallafi ko taron jama’a.
Lauyoyi da masu shahri da ’yan adawa sun bayyana abin da ya faru a matsayin abin takaici da ke nuna tsananin yunwa a tsakanin ’yan Najeriya.