✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen da Tinubu ya nada a Ma’aikatar Sadarwa

Tinubu ya ce sabbin shugabannin hukumomin da ke karkashin ma'aikatar sadarwa, da ya nada "sun fara aiki nan take".

Shugaba Bola Tinubu ya ce sabbin shugabannin hukumomin da ke karkashin ma’aikatar sadarwa, da ya nada “sun fara aiki nan take”.

Ga jerin mutanen da shugaban kasar ya nada kamar yadda kakakinsa, Ajuyi Nagalele ya sanar a ranar Laraba:

  1. Aminu Maida — Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC)
  2. Kashifu Inuwa Abdullahi — Shugaban Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa (NITDA)
  3. Nkechi Egerton-Idehen — Shugaban Hukumar Tauraron Dan Adam na Najeriya (NIGCOMSAT)
  4. Dokta Vincent Olatunji — Shugaban Hukumar Kare Bayanai ta Kasa (NDPC)
  5. Tola Odeyemi — Shugaban Hukumar Gidan Waya (NIPOST)
  6. Idris Alubankudi — Mashawarcin shugaban kasa kan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani.

“Shugaba Tinubu ya kuma umarce su da yi amfani da kwarewarsu a fannoninsu wajen bunkasa tattalin arzikin kasa,” in ji sanarwar.