Yawan fararen hula da aka kashe a harin da mayakan Al-Shabaab suka kai wani otel a Mogadishu, babban binin kasar Somaliya ya karu zuwa 13.
Wani jami’in tsaro ne ya sanar da hakan ranar Asabar a yayin a yake karin bayani kan kokarin ceto mutanen harin da mayakan suka kaddamar ranar Juma’a.
- Mayakan Al-Shabaab sun kashe mutum 8 a otel a Somaliya
- Kwamandan ’yan ta’adda zai auri fasinjar jirgin kasan Abuja-Kaduna
“Mun samu rahoto cewa an kashe karin mutane biyar, wanda ya sa yawan fararren hular da aka kashe karuwa zuwa 13,” inji kwamandan, mai suna Mohamed Abdikadir.
A ranar Juma’a ne mayakan Al-Shabaab suka kai hari otel din Al-Hayat da ke Mogadishu suna luguden wuta sunar tayar da ababen fashewa.
Maharan sun yi ta barin wuta har zuwa safiyar Asabar, inda suka yi garkuwa da otel din da mutanen da ke ciki.
Otel din Al-Hayat ya yi suna wajen karban bakuncin manyan mutane da jami’an gwamnatin Somaliya.
Jami’an tsaro sun yi nasarar kubutar da wasu daga cikin mutane da aka yi garkuwa da su.
Sun kuma zagaye wurin da mayakan suka kai hari da nufin kubutar da mutane da kuma murkushe ‘yan ta’addan.
Harin din otel din Al-Hayat din shi ne mafi muni a Somaliya tun bayan rantsar da sabuwar gwamnatin kasar a watan Mayu.