✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane sun mutu a turmutsitsin kallon wasan Kamaru da Comoros

Faruwar wannan al'amari bai hana an gudanar da wasan ba.

Kimanin mutum shida ne suka riga mu gidan gaskiya a wani turmutsitsin jama’a da ya auku a wajen wani filin wasanni da ake buga gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da ke wakana a Kamaru.

Gwamnan yankin Tsakiya na Kasar Kamaru, Naseri Paul Biya ne ya bayyana hakan a jiya Litinin da cewa akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutun ya karu.

Wannan turmutsitsin dai ya auku a yayin da jamaa suka rika kokawar samun damar shiga filin wasa na Olembe da ke Younde, babban birnin kasar domin kallon wasan zagayen ’yan 16 da ya gudana tsakanin Comoros da kasar ta Kamaru da ka zaman mai masaukin baki a gasar AFCON 2021.

Jaridar Wasanni ta Marca ta ruwaito mahukunta na cewa, an garzaya da akalla mutum 40 da suka jikkata zuwa asibitin Messassi wanda kuma cikinsu har da kananan yara da suka suma.

Wata malamar jinya a asibitin mai suna Olinga Prudence ta ce, “an kawo wasu da suka galabaita da ke bukatar kulawa cikin gaggawa, wanda tilas muka mika su zuwa wani babban asibitin kwararru.

Masu ruwa da tsaki a harkar tamaula sun ce mutum 50,000 ne suka yi kokarin shiga filin domin kallon wasan.

Haka kuma, bayanai sun ce filin wasan na iya daukar mutum dubu 60 ne, amma saboda matakan da mahukuntan lafiya suka gindaya na dakile yaduwar cutar Coronavirus, ba a yarda wadanda za su shiga filin ya haura kashi 80 cikin 100 na adadin da filin wasan zai iya dauka ba.

Ita kuwa NDTV ta ruwaito cewa mutum takwas ne suka mutu sakamakon turmutsitsin ciki har da mata biyu, maza hudu, karamin yaro daya da kuma wata gawa guda daya da ba a iya tantance jinsinta ba, sai kuma kimanin mutum 50 da suka jikkata.

An dai fafata a zagaye na biyu na gasar duk da faruwar wannan al’amari, wanda rahotonsa bai bulla ba sai bayan an tashi daga wasan.

A wasan ne dai kasar Kamaru ta yi nasara a kan Comoros da 2-1, da hakan ya ba ta damar tsallakawa zuwa zagayen Quater Finals a gasar.