Shugaban Ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya dakatar da ayyukan da aka shirya yi a Jihar Legas, domin girmama waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon turmutsutsin da ya auku a Abuja da kuma Jihar Anambra.
A Abuja, aƙalla mutum 19 ne suka mutu, ciki har da yara ƙanana, yayin da wasu da dama suka jikkata a sakamakon turmutsutsin da ya faru a wata cocin Katolika da ke unguwar Maitama.
Sanarwar da rundunar ’yan sandan Abuja ta fitar, ta bayyana cewa daga cikin waɗanda suka mutu akwai yara huɗu, yayin da mutum takwas suka samu munanan raunuka kuma yanzu haka suna karɓar magani a asibiti.
A Jihar Anambra kuwa, rahotanni sun ce wasu mutane sun mutu sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a wajen rabon tallafi a jihar a ranar Asabar.
Sanarwar fadar shugaban ƙasa, ta ce Tinubu, ya soke halartar kallon wasan kwale-kwale da aka shirya zai yi a Ikoyi, tare da yin addu’ar neman rahama ga waɗanda suka rasu da kuma fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
’Yan Najeriya dai, na fama da tsananin wahalar rayuwa sakamakon matakan tattalin arziƙi da gwamnatin Tinubu ta ɗauka.
Daga cikin matakan har da janye tallafin man fetur wanda ya haifar da tsadar kayan abinci da sufuri.