✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane na zanga-zangar adawa da dokar COVID-19 a New Zealand

Mutanen na neman a janye duk dokokin kariyar cutar COVID-19 a kasarsu.

Dubun dubatar mutane na zanga-zangar adawa da dokokin da aka kakaba na kariyar cutar COVID-19 a kasar New Zealand.

Fusatattun masu zanga-zangar sun yi wa ginin majalisar dokokin kasar tsinke domin nuna fushinsu ga dokar hana fita da aka sanya a kasar da kuma umarnin da gwamnati ta bayar na yin allurar rigakafin cutar domin hana yaduwarta a kasar.

Wani daga cikin masu zanga-zangar ya shaida wa manema labarai a kofar majalisar cewa, “Babu wanda zai tilasta ni a sanya min abin da ba na so ya shiga jikina.

“Abin da kawai nake so shi ne gwamnati ta bari abubuwa su ci gaba da gudana kamar yadda suke a 2018; So nake a dawo min da ’yancina.’’

Yawancin masu zanga-zangar da suka yi maci a tsakiyar birnin Wellington sun yi watsi da takunkuminsu na COVID-19, kafin daga karshe su yi burki a kofar shiga harabar majalisar.

Lamarin ya sa an sanya matakan tsaro da ba a taba ganin irinsa ba a harabar majalisar, inda aka rufe daukacin kofofin shiga face guda biyu.

Da yake jawabi a majalisar, Firai Ministan kasar, Jacinda Ardern, ya ce: “Abin da muka gani ba shi ba ne ra’ayin akasarin al’ummar New Zealand”.

Mista Ardern ya jima yana shan matsin lamba cewa ya sassauta dokokin na COVID-19, ganin cewa bukukuwan Kirsimeti na kara matsowa.

Kasar New Zealand na fadi-tashin murkushe naurin Delta na cutar COVID-19 da aka samu barkewarsa a kasar, lamarin da ya tilasta wa Firai Ministan sanya dokar hana fita kuma wajabta yin allurar rigakafi da zummar dakile yaduwar cutar.

A watan jiya, ya ce kasar na bukatar malamai da ma’akaikatan lafiya har ma da nakasassu su kammala karbar allurar rigakafin cutar a kasar.

Sai dai matakin ya jawo masa caccaka, inda jama’ar kasar ke cewa ’yancinsu suke bukata tare da neman a janye duk dokokin da aka sanya a kasar.

Har yanzu New Zealand na daga cikin kasashen duniya mafiya karacin yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19, inda mutum 8,000 suka kamu, daga cikinsu 32 suka rasu.

A ranar Talata an sanar da kamuwar karin mutum 125 da cutar, wadda zuwa yanzu sama da kashi 80 na ’yan kasar ne ake kokarin ganin sun karbi allurar rigakafinta.