Mazauna garin Maiduguri da ambaliya ta raba da muhallansu sun fara komawa gidajensu bayan ruwa ya fara raguwa a hankali.
Akasarin wadanda ambaliyar ta rutsa da su da suka kwana a waje sun ce ko da yake ruwan bai gama janyewa ba, suna son tantance asarar da suka yi.
Ali Bana na unguwar Gwange ya ce, “Muna saurin zuwa mu da abin da ya rage a gidajenmu da za mu iya daukowa na dukiyoyinmu da har yanzu za mu iya amfani da su.
Musa Abdullahi na unguwar Gomari, ya ce da ya je gidansa ya samu, “Har yanzu gidana yana cike da ruwa.
“Bisa dukkan alamu, za mu kara kwanaki a waje kafin mu koma ciki.”
Wani rahoton halin da ake ciki kan ambaliyar da Ofishin Kula da Ayyukan Kin Kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya ce fiye da mutane 239,000 ne ambaliyar ta shafa.
“Ambaliyar ta tilasta musu kaura zuwa sansanin ’yan gudun hijira na Muna, wanda tuni aka yi wa sama da dan Adam 50,000 rajista.
“Hukumomin gwamnati sun kwashe mazauna yankunan da ke da hatsarin kogin zuwa wurare da dama,” in ji rahoton.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ambaliyar ruwan ta shafi harkokin sadarwa, wutar lantarki da kuma samar da ruwan sha a galibin sassan garin Maiduguri.