✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutane na da ’yancin yin zanga-zanga – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci masu zanga-zangar #EndSARS da su kara wa Gwamnatin Tarayya lokaci domin ta samu biya musu bukatunsu. Ministan Bunkasa Wasanni…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci masu zanga-zangar #EndSARS da su kara wa Gwamnatin Tarayya lokaci domin ta samu biya musu bukatunsu.

Ministan Bunkasa Wasanni da Harkokin Matasa, Sunday Dare ya bayyana haka bayan ganawarsa da Buhari game da zanga-zangar da aka shafe sama da kwana 10 ana gudanarwa domin kawo karshen kama-karyar da ‘yan sanda ke yi a Najeriya.

Ministana ya ce tuni kwamitinin da Gwamnatin Tarayya ta kafa domin biyan bukatun matasan ta riga ta fara aiki.

Ya kara da cewa Shugaba Buhari ya kuma fahimci cewa masu zanga-zangar na da ‘yancin yin hakan domin neman biyan bukatunsu.

Sai dai ya bukaci masu zanga-zangar da su yi hattara kada bata-gari su saje da su, a yayin da suka neman biyan nasu bukatun.

Karin labarin na tafe..