Hukumomi sun tabbatar cewa mutane 22 ne suka samu raununa a sakamakon gobarar iskar gas a yankin Ajegunle da ke Jihar Legas.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce mutanen da gobarar ta ranar Talata ta ritsa da su suna samun kulawa a asibitocin gwamnati.
Gab da Azahar ce iskar gas ta yi bindiga, inda wasu mutane da dama suku makale a sakamakon tashin wutar.
Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya ce ba a samu asarar rai ba, kuma wadanda suka samu raununan suna samun sauki a inda ake kula da su.
Shi kuma kakakin hukumar kashe gobarar jihar, Amodu Shakiku, ya yi zargin cewa yoyon tukunyar iskar gas ce ta haddasa gobarar.
Jami’in ya bayyana cewa gobarar ta kone wasu shaguna shida da ke a rufe da kuma wani gida.