Mutane aƙalla 179 sun rasu wasu 208,655 sun rasa muhallansu a sakamakon ambiya a daminar bana a Najeriya.
Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta sanar cewa ambaliyar ta kuma lalata gonaki masu faɗin hekta 107,652da gidaje 80,049.
Rahoton da hukumar ta fitar ya bayyana cewa ambaliyar ta yi wannan ɓarna ce a jihohi 22 daga cikin 36 da Birnin Tarayya da ke Najeriya.
Ta ƙara da cewa jihohin Arewa ne akasarin inda aka samu ambaliyar, a sakamakon ruwan saman da aka samu a bana fiye da na daminar baya.
- Ƙuncin rayuwar ’yan Najeriya ce damuwata, ba takarar 2027 ba
- An yi wa almajirai 1,000 rajistar inshorar lafiya a Gombe
Yawan ruwan, a cewa rahoton ya yi sanadin cika da ambaliyar manyan kogunan Binuwai da Neja.
Ambaliyar a cewan rahoton ta faru ne a kananan hukumomi 137 a jihohi 28 da adadin mutanen da ta shafa kamar haka:
- Bauchi (86,000).
- Zamfara (75,000).
- Sakkwato (74,000).
- Jigawa (57,000).
- Neja (30,000).
- Kano (19,000).
- Imo (18,000).
- Adamawa (18,000).
- Ondo (17,000).
- Borno (17,000).
- Taraba (16,000).
- Kwara (12,000).
- Katsina (11,000).
- Yobe (11,000).
- Gombe (10,000).
- Benue (10,000).
- Legas (9,000).
- Enugu (8,000).
- Kaduna (7,000).
- Nasarawa (6,000).
- Bayelsa (5,000).
- Ekiti (4,000).
- Kebbi (4,000).
- Oyo (2,000).
- Kogi (2,000).
- Ebonyi (2,000).
- Akwa Ibom (2,000)
- Abuja 1,000).
Yawan mace-mace:
Jihar Jigawa ce ta fi rasa rayuka a albaliyar, da kuma sauran jihohi kamar haka:
- Jigawa (34).
- Bayelsa (25).
- Kano (25).
- Bauchi (23).
- Taraba (15).
- Zamfara (13).
- Sokkwato (10).
- Yobe (10).
- Adamawa (7).
- Katsina (5).
- Neja (5).
- Borno (2).
- Ebonyi (2).
- Kaduna (2)
- Nasarawa (1).
Asarar muhalli
Ta bangaren mutanen da suka rasa muhalli, Jihar Sakkwato ce kan gaba a cikin jerin jihohi 22, a cewar rahoton ambaliyar:
- Sakkwato (41,000)
- Bauchi (35,000).
- Zamfara (32,000).
- Neja (28,000).
- Jigawa (16,000).
- Imo (12,000).
- Taraba (8,000).
- Borno (7,000).
- Bayelsa (5,000).
- Enugu (4,000).
- Adamawa (3,000).
- Yobe (3,000).
- Nasarawa (3,000).
- Benue (2,000).
- Ondo (2,000).
- Katsina (2,000).
- Ebonyi (2,000).
- Gombe (1,000).
- Kebbi (1,000).
- Kano (1,000).
- Abuja (1,000).
- Kogi (1,000).
Gonakin da aka rasa
Faɗin hektan gonaki da aka rasa a jihohi 11 su ne:
- Bauchi (50,000).
- Taraba (21,000)
- Jigawa (10,000).
- Sakkwato (9,000).
- Neja (9,000).
- Kano (3,000).
- Zamfara (2,000).
- Gombe (1,000).
- Adamawa (1,000).
- Enugu (1,000).
- Kebbi (1,000).
Gidaje
Gidajen da ambaliyar ta lalata kuma jihar Bauchi ce a kan gaba;
- Bauchi (18,000).
- Sakkwato (10,000).
- Jigawa (8,000).
- Neja (7,000).
- Enugu (6,000).
- Borno (4,000).
- Zamfara (4,000).
- Kwara (3,000).
- Kano (3,000).
- Yobe (3,000).
- Katsina (2,000).
- Ondo (2,000).
- Kogi (2,000).
- Kaduna (2,000).
- Oyo (1,000).
- Imo (1,000).
- Gombe (1,000).
- Kebbi (1,000).
- Abuja (1,000).
Shugabar hukumar NEMA, Zubaida Umar, a yayin ganawa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, wanda ya ziyarci hukumar cewa NEMA ta riga ta tantance girman barnar da ambaliyar ta yi a kusan duk jihohin da abin ya shafa.
Ta ce babban ƙalubalen shi ne yadda hukumar za ta gudanar da ayyukan da ke gabanta.
A nasa ɓangaren, Gbajabiamila ya ba da shawarar a kafa dokar dame da kuɗaɗen haɗaka tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi domin gudanar da ayyukan Hukumar NEMA.