✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulunci ke ba da ’yanci na hakika

Daga Hudubar Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-HusainMasallacin Sharif Ibrahim Saleh, Gwange, Maiduguri Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonsa, muna neman…

Sheikh Sharif Ibrahim SalehDaga Hudubar Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Husain
Masallacin Sharif Ibrahim Saleh, Gwange, Maiduguri

Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonsa, muna neman gafararSa, muna tuba gare Shi, muna rokonSa a kowane lokaci muna masu daga hannuwa cikin kankan da kai gare Shi. Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma Y abatar ba za ka sama masa wani majibinci mai shiryarwa ba.
Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare shi, Mamallaki, kuma Gaskiya Mabayyani. Kuma na shaida shugabanmu, jagoranmu, abin girmamawarmu, mai cetonmu kuma Annabinmu Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa ne (SAW), mai cika alkawari, amintacce. Allah Ya aiko shi da shiriya da addinin gaskiya don rinjayar da shi a kan duk wani addini. Ya Allah Ka kara tsira da aminci da albarka a kansa da alayensa tsarkaka da shabbansa jagororin masu jihadi na hannun damansa yardar Allah ta tabbata a gare su baki daya.
Bayan haka, lallai Allah (TWT) Yana cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa a kan hakkin binSa, kuma ku yarda ku mutu face kuna Musulmi. Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada ku rarraba.”  (Al-Imrana: 102-103). Kuma Ya sake cewa: “Kada ku yi jayayya ku tarwatse karfinku ya tafi. Ku yi hakuri, lallai Allah Yana tare da masu hakuri.” (Al-Anfal: 46).
’Yan uwana a tafarkin Allah! Lallai duniyarmu tana gudana a bisa wani tsari mai mugun hadari. Ba duniyar Larabawa kadai ba, duk kasashen Musulmi suna fama da wannan bala’i. Muna cikin wani bala’i da aka assasa shi a karkashin wani tsari da ake kira dimokuradiyya. Wannan tafarki har abada ba zai kai mu ga gaci ba matukar muka bi shi yadda Turawan Yamma suka tsara. Gaskiyar abin da ke akwai babu dimokuradiyya hatta daga wadanda suke riya cewa su ne asalin dimokuradiyya. Su ne suka assasa ta, kuma su ne masu kira zuwa gare ta, kuma su ne masu kyautata ta. Dimokuradiyya kamar yadda wadannan mutane suke siffanta ta ba a samunta hatta a Amurka da Birtaniya, kuma ba a samunta har abada a wata kasa ta duniya. Idan hakikanin dimokuradiyya na nufin yin adalci da aiki da shawarwari ne, to ba za a samu wannan dimokuradiyya ba, sai a karkashin tsari daya, shi ne tsarin Musulunci.
Musulunci ya ba kowane mai hakki hakkinsa, mutum ya samu hakkinsa a karkashin Musulunci, dabbobi ma sun samu hakkinsu a Musulunci. Kowane mai hakki ya samu hakkinsa a Musulunci. A Musulunci kowane mutum na da wani nauyi a kansa. Kowanenku abin tambaya ne a kan kiwon da aka ba shi. Kowane mutum daga cikin Musulmi na da hankali daga Allah da kuma fahimta, kuma abin umarni ne bisa muradin Allah. Kuma Musulmi ne yake kwatanta umarce-umarcen Allah da hane-hanenSa. Kuma kamar ga shi kadai ne aka aiko Manzanni aka saukar masa da littaffai, yana kwatanta aiki da Alkur’ani. Kuma kamar shi kadai ne ake nufi da tsayar da wadannan wajibai, yana imani da Manzon Allah (SAW), kuma a cikin haka yana imani da dukkan Manzanni da Annabawa. Yana karbar umarni daga gare shi (SAW) yana aiki da shi, yana sauraron hane-hanensa yana guje musu. Yana aiki da dukkan wadannan ababen da’a da dalilai na shari’a, kai ka ce shi kadai aka umarta da haka. Ba ya taraddudi kuma bai tsayawa ga biyayya ga wasu, iyaka duk abin da ya ji sai ya bi, saboda sanin cewa wani kebabben al’amari tasirinsa a kan rai ya fi karfi da girma a kan aiki na umumi. Domin idan ka umarci jama’a da wani al’amari su aikata shi, ta yiwu wasu su yi sakaci su ce wasu za su yi, su kyale wasu su yi. Sabanin da za ka umarci mutum ka ce: “Wane yi kaza.”
Musulmi mai hankali ba makawa ya sanya rayuwarsa a wannan matsayi. Ya rika ganin kamar shi kadai aka halitta, ya kasance shi kadai a cikin mahaifiyarsa, aka haife shi shi kadai, kuma yana rayuwa a wannan duniya a kan kansa shi kadai. Yana ji a jikinsa da tunaninsa cewa shi kadai ne ba wanda yake tarayya da shi a ciki haka. Kuma a barzahu shi kadai ne, sannan a tashe shi, shi kadai, a yi  masa hisabi shi kadai, sannan ya yi sa’ada ko ya tabe shi kadai. To idan haka al’amarin yake wajibi ne a kansa ya rika ganin kansa cewa abin tambaya ne a kan komai shi kadai.
Wannan kasa tamu mai mulki da wanda ake mulka, babba da yaro suna shagala da batun zaben wanda zai mulki kasar nan, wanda ya fi cancanta da wanda ya fi dacewa. Wannan idan ma an samu zaben share fage da zaben gama-gari na gaskiya mai adalci ke nan. Idan kuma ba a samu haka ba, babu abin da zaben zai iya kawowa cikin abin da ake nufi da shi ko ake nufin ya kawo, kuma wannan shi ne abin da ke faruwa a kasashe da dama.
A zaben da ya gabata a kasar nan, bayan fadin sakamakon zaben an samu rarrabuwa a tsakanin ’yan Najeriya, wasu mutane ba su amince da sakamakon zaben ba, yayin da wasu suka amince, me ya kawo haka, an bar ginshiki ko tushe.
Na farko: Imani ingantacce.
Na biyu: Amincewa a tsakanin mutane.
Idan aka samu imani yana hukuta mutum yana tsara tasarrufinsa yana hukunta abin da zai tsayu a kai da abin da zai yi, babu shakka wannan zai haifar da amincewa da shi a zuciyar sauran jama’a, a samu yakini da abin da zai ce, sai a cimma muradi. Sai dai kash, imanin mai rauni ne, an kuma rasa amincewa a tsakanin mutane. Duk lokacin da wani ya ce, sai wani ya kalubalance shi, wannan ne yake jawo tashe-tashen hankula a wurare da dama a wannan kasa da suke haifar da zubar da jini da kashe rayuka da lalata dukiya da korar matasa da dama ko kame su ana sanyawa a kurkuku, kuma abin bakin cikin korar da kame-kamen suna aukuwa a bangare daya.
Don haka muna kira ga wadanda alhakin gudanar da al’amura ke hannunsu su dubi gaba kada su duba baya, su dubi makomar kasar nan. Allah Madaukaki ta sanya wannan kasa ta Musulmi da wadanda ba Musulmi ba da suke waste a sassan kasar nan Kudu da Arewa, Ya nufe mu mu rayu a haka cikin hikima. Sannan kowane bangare ya rika karfafa mu wajen ci gaba da hidima ga addininmu da hidima ga jama’armu. Ma’ana iradar Allah ta hukunta mu rayu tare, don haka babu makawa mu watsa abubuwan da za su kawo zaman lafiya a tsakaninmu. Bai halatta ga wani bangare a wannan kasa ya tauye wani bangare har ya kai shi ga bango ba.
Ya wajaba mu rayu gaba daya mu riko da addinimu, bai halatta ga waninmu ya ce, tunda wane bai yi adalci ba, ni ma ba zan yi adalci ba, a’a ya wajaba a kan Musulmi ya kasance Musulmi a cikin wahala ko kunci, Musulmi a cikin yalwa ko wadata, Musulmi a lokacin zalunci, Musulmi a lokacin adalaci.