✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulmin Kaduna sun yi biris da shawarar El-Rufai

Galibin masallatai a birnin Kaduna sun yi watsi da shawarar da gwamnati ta bayar cewa kada a gudanar da sallar Juma’a. Wadansu daga cikin masallata…

Galibin masallatai a birnin Kaduna sun yi watsi da shawarar da gwamnati ta bayar cewa kada a gudanar da sallar Juma’a.

Wadansu daga cikin masallata wadanda Aminiya ta zanta da su dai sun ce ba su ma san gwamnatin ta bayar da shawarar ba sai a kan hanyarsu ta zuwa masallaci.

Gwamnatin ta bayar da shawarar ne dai a wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mai bai wa Gwamna Nasir El-Rufai shawara a kan al’amuran sadarwa da yada labarai, Muyiwa Adekeye, da nufin takaita yiwuwar yada cutar Coronavirus ta hanyar taruwar dimbin jama’a.

Sanarwar ta ce hukumomin na yi koyi ne da shawarar da Saudiya ta yanke cewa ba za a yi sallar Juma’a a Masallacin Harami da Masallacin Annabi ba.

“A kasashen Musulmi da yawa irin su Saudi Arabia, da Kuwait, da Hadaddiyar Daular Larabawa, an karfafa gwiwar al’umma da su yi salla a gida, a maimakon su yi jam’i kamar yadda aka saba”, inji Mista Adekeye.

Sai dai ba a taru aka zama daya ba, wadansu masallatan ba su gudanar da sallar Juma’ar ba.

Wadannan masallatai sun hada da Masallacin Juma’a na Ansaruddeen da ke Abeokuta Street, da Masallacin Nawarul Failat, da kuma Masallacin Nurudeen.

Rahotanni sun ce masallatan ba su yi sallar ba ne saboda tuni da ma uwar kungiyar Ansaruddeen ta kasa ta fitar da sanarwa tun da sanyin safiyar ranar Juma’a tana umarnin kada a gudanar da sallar cikin jam’i.

Sanarwar gwamnatin jihar ta Kaduna ta kuma yi kira ga majami’u da su ma su rufe kofofinsu ranar Lahadi.

“Ana sa rai cewa daga fastoci har zuwa masu bi kowa zai yi aiki da wannan shawara ta kiyaye lafiyar al’umma su guje wa taruwa a majami’u. kamata ya yi sauran nau’uka na ibada kada a tara fiye da mutum 10 yayin gudanar da su”, inji sanarwar.

Bugu da kari sanarwar ta ce an dakatar da duk wani taron jama’a, kama daga bukukuwa zuwa taruka a mashaya, ko gidajen cin abinci, ko gidajen rawa, ko wasu wurare masu kama da su, har sai abin da hali ya yi.