✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin zarafi ba zai hana ni tsage gaskiya ba —Danbilki Kwamanda

“An sanar da ni mutanen gwamnatin na nema na su ci min mutunci. Ni ne na uku [da suka yi wa haka],” in ji shi

Fitaccen dan siyasa a Jam’iyyar APC, Abdulmajid Danbilki Kwamanda, ya bayyana cewa cin zarafin da aka yi masa ba zai sa ya daina tsage gaskiya ba, musamman ga ’yan jam’iyyarsa.

Danbilki Kwamanda ya kuma karyta gwamnatin Kaduna da ke nesanta Gwamna Uba Sani da wani bidiyon cin zarafi da aka yi wa dan siyasar kan sukan gwamnan.

A hirarsa ta musamman da Aminiya, kan lamarin, Danbilki Kwamanda ya ce, “Ina nan ba zan canza ba, kuma wannan abin da ya faru gare ni, Wallahi kamar an yi min allura ne.”

Ya ci gaba da cewa, ko kafin a yi masa wannan aika-aika da sama da mako guda, “an sanar da ni mutanen gwamnatin na nema na su ci min mutunci. Ni ne na uku [da suka yi wa haka].”

Ya ci gaba da cewa, a matsayinsa na wanda ya tallata Uba Sani da Jam’iyyar APC da sauran ’yan takararta, har suka kafa gwamnati a matakai daban-daban, yana da hakkin yi musu gyara duk inda ya ga sun yi kuskure.

A wani bidiyon da ya karade gari, an ga wasu mutane sun tsare dan siyasar a cikin dare da ankwa a hannunsa, inda suka rika yi hantarar sa suna masa bulala saboda a cewarsu ya zagi gwamnan Kaduna.

A cikin hirarmu da shi, Danbilki Kwamanda ya fede biri har wutsiya game da abin da ya faru da shi da inda ya samo asali da kuma inda aka kwana.

Za mu saki bidiyon cikakkiyar hirar anjima kadan a shafukanmu na Youtube da Facebook da TikTok.