Sama da musulmi 500 suka halarci gidan Fasto Yohanna Buru a Kaduna don taya shi da sauran kirista murnar bikin kirsimeti, ziyarar zata kara dankon danganta tsakanin mabiya addinan biyu wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Matasa maza da mata, limamai da kungiyoyi masu zaman kansu da sarakuna daga sauran jahohin Arewacinauran jahohin Arewacin Najeriya da makwabta qasar ne suka halarci gidan Faston a Kaduna.