Daga Nasir Abbas Babi
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai.
Musulunci addini ne nagari, kuma addini na gaskiya da ma’abutansa ya kamata su yi alfahari da samunsa a matsayin addini. Wannan ne ya sanya duk wanda yake kiran kansa Musulmi, ransa yakan baci matuka idan ka kira shi da wani suna da ke nuna cewa shi ba Musulmi ba ne. Kamar ka kira shi da arne ko kafiri ko mushriki da sauransu.
Sai dai ba kowane Musulmi ne cikakken mumini ba, kuma ba kowane Musulmi ne ke iya amsa sunan Musulmi nagari ba. Amma dai duk Musulmi, yana nan a matsayinsa na Musulmi kuma cikin lemar Musulunci, matukar bai aikata wani aiki ko ya furta wata magana da Allah da ManzonSa suka tabbatar da aikin ko kuma maganar sun fitar da wanda ya yi daga Musulunci ba.
Musulunci addini ne na Allah. Don haka babu mai hurumin korar wani daga ciki, sai dai shi mutum ya kori kansa, ko kuma idan shari’ar Allah ta kore shi, (saboda saba mata).
Musulmi nagari shi ne, mai wankakkiyar zuciya, (kubutacciya daga shirka da sabo) mai cike da aminci. Ya kasance ba ya nufin kowa da sharri sai dai soyayya. Saboda addinin Musulunci bai yarda ka cutar da koda mutum marar addini ba, balle Kirista ko Yahudu. Koyaushe Musulmi nagari za ka same shi mai son ci gaban al’umma ne ba mai neman tarwatsewarta ba. Koyaushe zai kasance a cikin yin maraba da annashuwa ga sauran jama’ar da ya sansu ko bai sansu ba.
Musulmi nagari, shi ne wanda ya kasance mai horo da aikata alheri da hani ga aikata sharri. Kuma ya kasance mai karbar horo idan an hore shi da aikata alherin, kuma mai hanuwa idan an hane shi ga aikata sharri. Ya kasance mai kamanta adalci da tsare gaskiya a cikin huldarsa da sauran al’umma. Musulmin kirki ne yake kasancewa tamkar mabubbuga ta alheri ga mutane, yana mai burin koyaushe al’umma su karu da alherukansa. Kuma ya kasance mai taushin zuciyar da take cike da tausayi ga al’umma.
Musulmi nagari, shi ne Musulmin da bai kasance juji matattarar shara ba! Wato bai yarda ya wulakanta kansa da sunan tawali’u (kaskantar da kai) ba. Wajibi ne ya kasance mai nuna girmansa da kimarsa ga duk wanda yake ganin cewa shi babba ne ko kuma ya isa dole a yi masa biyayyar (da ta saba wa shari’a). A irin wannan hali, Musulmi ba zai wulakanta kansa ba, ba zai sassauta ba, ba kuma zai daga kafa ba, ba zai yarda ya bar kafar raini ba. Duk wani mai girman kai da jiji da kai, bai dace a samu Musulmin kirki yana yi masa biyayya a kai ba.
Musulmi nagari shi ne wanda zai kasance tamkar ruwa saboda saukin lamarinsa, kuma ya zamo tamkar takobi gaya-wa-jini na-wuce saboda kaifinsa! Ya kasance tamkar tauraruwa mai haske ga al’umma, kuma idan an zo fagen bayar da shaida ko fadar gaskiya, ya zamo tamkar makaho ta yadda ba zai gane nasa ko wanda ba nasa ba. Ana so Musulmin kirki ya kasance hasken da ke haskaka al’umma, a gefe daya kuma ya zamo tamkar wuta mai zafi da kuna.
Musulmi nagari shi ne wanda ya rike Littafin Allah sau da kafa, yana mai shaidar cewa babu wata shari’a mafificiya a kan shari’arSa (Allah). Kuma Annabi Muhammad (Mai tsira da amincin Allah) ya kasance abin koyinsa a dukkan al’amurra! Ya rike dukkan Musulmi a matsayin ’yan uwansa da yake iya bai wa kariya a kowane lokaci. Ya kuma rike tsoron Allah ya kasance masa garkuwa kuma guzuri a kowane lokaci.
Musulmi nagari shi ne Musulmin da zuciyarsa ta kasance cike da tsoron Allah. Ayyukansa da zantukansa suka kasance a cikin ambaton Allah dare da rana. Ya kasance mai fara kowane al’amari da ambaton sunan Allah, idan kuma ya cika ya kasance mai godiya ga Allah! Koyaushe ya zamo mai kwadayi da neman Allah Ya shiryar da shi zuwa ga hanya madaidaiciya, bisa ga kasancewar duk yadda kake ganin kamar kana rayuwa a kan gaskiya, ba lallai ba ne ya kasance a wurin Allah ma haka kake.
Musulmi nagari shi ne wanda rayuwarsa ta kasance yana yin ta ne saboda Allah Shi kadai, ba wanda yake rayuwa saboda wasu bururruka na duniya da ya saka a gabansa ba. Ya kasance mai fatar idan mutuwarsa ta zo, ta kowace hanya ce ta kasance a kan tafarkin Allah ne kai-tsaye. Musulmin kirki yakan kasance ba ya tsoron kowa sai Allah. Ba ya neman kowace alfarma ga wani dan Adam face Allah!
Wannan hanyar ita ce hanyar gaskiya! Ita ce hanyar Allah marar kwana ko lungu! Ita ce hanyar da kowane mutum ya kamata ya kasance a kanta. Wanda kuma ya dauki wata wadda ba ita ba, kuma har yake ganin idan ba an bi ta ba, to, ba za a dace ba, lallai ya zo da wani al’amari na daban. Kuma ya bi hanyar da ba za ta fitar da shi ba. Babu wanda aka ce dole a bi shi sai Manzon Allah (SAW)! To amma kuma ba za ka san Manzon Allah (SAW) ba sai ka je makaranta. Don haka, Musulmi mu koma makaranta. Kafirta juna da zagin magabata ba aikin Musulmin kirki ba ne.
Cikakken Ahlus Sunna shi ne, wanda yake biye da dokokin Allah sau da kafa a kan hanyar Manzon Rahama (SAW). Shi kuma dan bidi’a shi ne mai take Hadisin Manzon Allah (SAW) ingantacce idan ya saba wa tunaninsa ko akidarsa. Don haka a kowane lungu da sako na Musulmi akan samu Ahlus-Sunna kuma akan samu ’yan bidi’a.
Jama’ar Musulmi mu koma makaranta. Ya Allah Ka sanya mu cikin Musulmi nagari da ke kan sunnar Manzon Allah (SAW).
Nasir Abbas Babi,
Ya aiko wannan rubutu ne daga Sakkwato kuma za a iya samunsa ta waya mai lamba:
08033186727