Masallacin Juma’a na Al-Mukil
Fassarar Salihu Makera
Daga cikin darussan dogaro ga Allah a lokacin tsanani, akwai abin da Annabi (SAW) ya sanar da Sayyidina Usman bin Affan (RA), lokacin da ya yi masa bushara da Aljanna kan jarrabawa ko bala’in da zai same shi. Sayyidana Usman bai kara da komai ba, face cewa, “Allahu Musta’anu- ma’ana Allah ne Mai taimako, Ya Ubangiji Ka ba ni hakuri, kuma ga Allah na dogara.” Ahmad ya ruwaito.
Lallai bai tambayi Annabi (SAW): “Yaushe jarrabawar za ta kasance ba? Ko yaya za ta kasance? Bai damu da sanin nau’inta ba, ko su wane ne za su jawo ta ba. Abin da ya damu da shi daya ne, shi ne guzurin yadda zai fuskanci wannan bala’i da kuma neman taimakon Allah a cikin wannan tsanani. Ya damu da neman taimakon Allah Madaukaki da dogara a kanSa. Kuma lokacin da bala’in ya iso sai Allah Ya taimake shi, ya tabbata a cikinsa ya tsallake shi da mafi kyan zabi. Domin an tsare shi a gida amma bai girgiza ba, sai ya zamo tabbatarsa da cijewarsa sun taimaka wajen kare zubar da jinin Musulmi, har Khawarijawa suka kashe shi yana mai fatar rahamar Allah, ya samu tabbata ce albarkar addu’arsa da neman taimakon Allah Madaukaki da dogaronsa ga Allah lokacin da ya samu labarin za a jarrabe shi.
Ya ku bayin Allah! Muna da abin koyi mai kyau daga masu tawakkali, domin Allah Madaukaki lokacin da Ya ba da labarin tawakkalin Annabi Ibrahim (AS) da yadda ya fuskanci al’ummarsa da yadda ya barranta daga gare su, sai ayar ta fara da fadin Madaukaki: “Hakika abin koyi mai kyau ya kasance a gare ku game da (rayuwar) Ibrahim da wadanda suke tare da shi.”Kuma Allah Ya kammala ayar da cewa: “Ya Ubangijinmu a gare Ka muka dogara, kuma gare Ka muke juyowa kuma gare Ka makoma take.” (Mumtahanna: 4). Don haka mu zamo kamar yadda suke, mu nuna tawakkali a lokutan da masifu da sauran abubuwa masu tsoratarwa suka same mu. Domin Allah Madaukaki Ya shaida wa AnnabinSa (SAW) cewa: “Ya kai Annabi! Allah ne Ma’ishinka, kai da kuma wanda ya bi ka daga muminai.” (Anfal:64). Allah Yana isar mana idan muka yi tawakkali gare Shi.
Ya Ubangiji! Ka cika zukatanmu da imani da yakini a gare Ka da dogaro gare Ka da komawa zuwa gare Ka da yarda da Kai kuma Ka yardar da Mu, Ka yardar da mu, Ka kare mana bala’i kuma Ka kare Musulmi daga bala’i, ya Ubangijin talikai.
Huduba ta Biyu:
Hamdala da taslimi.
Bayan haka, ku bi Allah da takawa ku yi maSa da’a. Ku sani abubuwan da Allah Ya kaddara game da ibada sun wuce, kuma hukunce-hukuncenSa a cikinsu masu gudana ne, kuka ba ya mayar da su, kuma babu mai gudu daga gare su. Sai dai mumini ya nemi taimakon Allah a kansu, a karfafa zukata da tawakkali da komawa ga Allah Madaukaki ta wajen tuba da ibada da addu’a. “Ka ce: “Babu abin da zai same mu, sai abin da Allah Ya hukunta mana. Shi ne Majibincinmu, kuma ga Allah sai muminai su dogara.” (Tauba:51).
Ya ku Musulmi! Tawakkali shi ne gaskiyar dogarar zuciya ga Allah Madaukaki wajen jawo abin amfani da tunkude cuta na daga al’amuran duniya da Lahira baki daya. Da yawa mutum kan rudu cewa yana dogaro ga Allah, alhali shi mai dogaro ne da wadansu sabubba, ko yana dogaro da wasu halittu. Hakika ya zo cikin Hadisi: “Wanda ya ta’allaka da wani abu, an jingina shi gare shi.” Tirmizi ya ruwaito.
Ya wajaba ga mumini ya rika ji a zuciyarsa cewa abu mafi girma a wurinsa shi ne addininsa da kuma neman yardar Ubangijinsa. Ya fifita haka a kan komai na duk abin so kamar matansa da ’ya’yansa da dukiya da daukaka. Kai ya dauka duniya gaba dayanta a wurin mumini ba ta kai darajar addininsa ba. Domin haka a lokacin fitina da rashin zaman lafiya da zaman tsoro da firgici, wajibi ne a kan mumini kada wani abu ya shagaltar da shi ya kasa tabbatar da ransa da iyalansa da ’ya’yansa a kan addininsa. Domin duniya mai gushewa ce da farin cikinta da jin dadinta, babu tabbata sai a gidan Lahira, babu sa’ada ga mutum a cikinta sai ta hanyar tabbata a kan addini.
Yana daga cikin masu tawakkali, wanda ya yi tawakkali ga Allah wajen neman wani abu na duniya ko kiyaye shi, sai Allah Madaukaki Ya ba shi abin da Ya yi nufi sakamakon tawakkalinsa gare Shi, sai dai ya rasa abin da ya fi girma da daraja, shi ne tawakkali ga Allah Madaukaki wajen tsare addininsa da tabbata a kansa da kiran mutane zuwa gare shi.
Ibnul kayyim (Rahimahullah) ya ce: “Mafi falalar tawakkali shi ne yin tawakkali a cikin wajibi, wato wajibin Allah da wajibin halitta da wajibin kai. Mafi yalwa kuma mafi amfaninsa, shi ne tawakkali wajen tasiri na fili don kyautata addini ko tunkude fasadi daga addininsa. Wannan shi ne tawakkalin Annabawa (AS) wajen tsayar da addinin Allah da kawar da fasadi a bayan kasa. Kuma wannan shi ne tawakkalin magadansu, sannan sauran mutane a bayansu wajen tawakkali suna bibiyar juna ne gwargwadon himma da manufofinsu. Daga ciki akwai mai tawakkali ga Allah domin ya samu mulki da wanda yake tawakkali domin samun wani abin duniya.”
Kuma duk yadda jarrabawa ta kai ga girma, duk yadda bakin cikin ya kai ga tsananta, duk yadda bala’i ya rika bibiyar juna, to, lallai masu tawakkali sukan tabbata a kan addininsu, wani abu ba ya kawar da su. Sukan samu sa’ada daga rahamar da take tare da su, suna jin sa’ada a lokacin da suke tsakiyar bala’i, har ya zamo wadansu su fi su jin tsananin abin da ya same su, alhali su suna cikin natsuwar da ba ta siffantuwa. “Duk wanda ya dogara ga Allah, to, Shi (Allah) Ya isar masa. Lallai Allah Ya cika al’amarinSa, kuma hakika Ya sanya wa komai gwargwado.” (dalak:3).
Saboda muhimmancin tawakkali ga rayuwar mumini, sai ya zamo an wajabta masa yin addu’a a kowane lokaci, daga cikin addu’o’in akwai na fita daga gida, domin mai fita daga gida bai san me zai auku da shi ba na bala’i da fitina ba. Hakika Annabi (SAW) idan zai fita daga gidansa daga cikin addu’o’in da yake yi akwai: “Bismillahi tawakkaltu alallahi.” Kuma sakamakon wannan tawakkali shi ne kiyayewa da tsarewa ga mutum kamar yadda Annabi (SAW) ya ce: “Idan mutum ya fita daga gidansa sai ya ce: “Bismillahi tawakkaltu allallahi, wala haula wala kuwwata illa billah.” Ya ce : “A lokacin za a ce: “Ka shiryu kuma an kiyaye ka, kuma an kare ka. Sai shaidanu su yi kururuwa. Sai wani shaidani ya ce: “Yaya za ka yi da mutumin da ya shiryu kuma aka tsare shi kuma aka kare shi?” Abu Dawuda ya ruwaito shi, kuma Ibnu Hibban ya inganta shi.
Don haka ya bayin Allah! Mu kiyaye wannan zikiri mai albarka, kuma ya kasance mafi muhimmancin manufarmu wajen tawakkalinmu ya zamo tsare addininmu, sannan kyautata duniyarmu, domin kyautatuwar duniya na taimakawa wajen tsare hakkokin Allah Madaukaki da hakkokin bayinSa a kanmu. “Ya Ubangijinmu! Gare Ka muka dogara, kuma gare Ka muke tuba, kuma gare Ka makoma take. (Mumtahanna:4).