Lauyoyi Musulmai daga Jihar Sakkwato sun yi barazanar kaurace wa taron Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), saboda janye gayyatar Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da kungiyar ta yi.
Shugabannin Kungiyar Lauyoyi Musulmi reshen Jihar Sokoto sun ce reshen ba zai su halarci taron na ranar 26 zuwa 29 ga Agustan 2020 ba, har sai NBA ta gayyaci El-Rufai.
- Soke gayyatar El-Rufai: Lauyoyin Jigawa za su kaurace wa taron kasa
- Janye gayyata: El-Rufai ya caccaki kungiyar lauyoyi
- El-Rufa: Majalisar Shari’a ta caccaki kungyar NBA
Ana iya tunawa kungiyar ta soke gayyatar gwamnan ne a matsayin daya daga cikin masu jawabi a taron, saboda wasu ‘ya’yanta sun yi barazanar kaurace wa taron.
Wadanda suka yi barazanar ta farko sun zargi gwamnan da take hakki da rashin magance kashe-kashe a yankin Kudancin Jihar Kaduna da kuma saba umarnin kotu.
Soke gayyatar da kungiyar ta yi haifar da muhawara tsakanin magoya baya da masu suka, ciki har da manya lauyoyi da kwararru daga sassa daban-gaban.
A ranar Litinin, lauyoyin Musulmin sun ce NBA ba ta yi wa El-Rufai adalci ba domin sauran masu jawabi a taron ma ana zarginsu da saba umarnin kotu da dokar kasa.
“Amma aka bar su su yi jawabi a taron wanda hakan ya saba ka’idar adalci na sauraron mai zargi da wanda ake wa zargi, wanda shi ne tubalin hukunci.
“Kamata ya yi ta kyale El-Rufai ya halarci taron duba da maudu’in da za a tattauna, ko kuma ta janye gayyatar sauran masu jawabin”, inji Shugaban Kungiyar Lauyoyi Musulmi a Jihar Sokoto Muhammad Aliyu da Kakakin kungiyar Muhammad Abubakar.