✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mustapha Waye: Abubuwa 3 da za a rika tunawa da Daraktan ‘Izzar So’

Ko a ranar da zai rasu sai da ya yi karatun Qur’ani da Dala’ilu kamar yadda ya saba a kullum.

A karshen makon da ya gabata ne Allah Ya yi wa Daraktan fim mai dogon zango na “Izzar So” Nura Mustapha Waye rasuwa.

Jarumin fim din na “Izzar So” Lawan Ahmad ne ya bayyana rasuwar Nura a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi.

Nura Mustapha, darakta ne da aka dade ana damawa shi a masana’antar ta Kannywood.

Fim din na Izzar So na daga cikin fina-finai masu dogon zango da suka fi karbuwa a tsakanin masu bibiyar fina-finan masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya.

Kiyasi da aka yi a baya-bayan nan, ya nuna cewa fim din shi ne ya fi yawan masu kallo a dandalin YouTube da ake nuna fim din.

A wata hira da Aminiya ta yi da Balarabe Tela, wani dan uwa ga marigayin kuma tsohon jarumi a Kannywood, ta samu jin wasu abubuwa guda 3 da za a rika tunawa dangane da marigayi Nura Mustapha Waye.

Ya dade a masana’antar shirya fina-fanai ta KANNYWOOD:

Izzar So ba shine fin na farko ba na Marigayi Nura Mustapha ba. Marigayin ya dade da shiga masana’antar ta Kannywood tun shekarar 2001. Ya  kuma yi fina-finai da dama.

Lakabin WAYE a sunansa

Ana yi wa marigayin lakabi da WAYE ne saboda da shi ne fim dinsa farko, wanda a bisa al’adar ‘yan masana’antar ana yi wa mutum lakabi da wani fim da ya fara yi, ko kuma ya yi suna a cikinsa.

Ilimin addini da kuma mu’amalla ta gari

Marigayi Nura makarancin Al kura’ni ne da kuma littafina yabo na manzon Allah (SAW) Dala’ilu khairat.

A cewar Balarabe Tela, “ko a ranar da zai rasu sai da ya yi karatunsa na Qur’ani da Dala’ilu kamar yadda ya saba a kullum.

“Sakamakon ilimin addini da ya taso da shi Hakan kuma ya tasirantu matuka a fim dinsa na Izzar So.”

Balarabe ya kuma ce, marigayin ya na da mu’amala mai kyau da jama’a, ba wai a Kannywood ba, hatta a unguwarsu ta Goron Dutse mutane sun ji rasuwarsa sosai soboda kyakkyawar mu’amallarsa.

Nura Mustapha ya arasu ne a ranar Lahadi da safe, tuni aka yi jana’izarsa a unguwarsu ta Goron Dutse a Kano, kamar yadda musulunci ya tanada.