✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muryar Talaka ta kafa kwamitin sasantawa a Kano

kungiyar Muryar Talaka ta yi babban taro domin samar da ingantacciyar hanyar dawo da shugabanci mai nagarta ta yadda za ta ci gaba da gwagwarmayar…

kungiyar Muryar Talaka ta yi babban taro domin samar da ingantacciyar hanyar dawo da shugabanci mai nagarta ta yadda za ta ci gaba da gwagwarmayar da take yi na kyautata jagoranci a kasa da kare martabar talakawan Najeriya kamar yadda manufofin kafa ta suke.

Taron wanda ya gudana a dakin karatu na Murtala Mohammed dake birnin Kano, ya sami halartar shugabannin kungiyar 11 daga cikin shugabanni 16 da kungiyar ke dasu, tare da mambobi daga jihohi daban-daban na dukkanin rassanta, inda aka tattauna muhimman al’amura da suka shafi martabar kungiyar da kuma tabbatar da ganin an dawo mata da shugabanci wanda kowa zai amince da shi. Haka kuma anyi jawabai masu ma’ana tare da gabatar da hujjoji na bukatar samar da shugabanci bisa tsarin mulkin kungiyar da tabbatar da bin ka’idoji wajen zabar shugabannin da za su ci gaba da jan ragamarta kamar yadda yake a bayyane, sannan daga karshen taron aka kafa kwamitoci guda biyu watau kwamitin rikon kwarya mai mutane bakwai da kuma kwamitin sasantawa shi ma mai mutane bakwai domin ganin an shirya ingantaccen zabe wanda zai gamsar da kowane dan kungiya dake fadin wannan kasa.

An dai nada Sagir Musbahu Daura a matsayin shugaban kwamitin rikon kungiyar da shirya zabe, sai Nasir B. Sherif Gombe a matsayin sakatare da Isa Ramin Hudu Hadejia a matsayin jami’in hulda da jama’a, sai Bilya G. Aliyu Gusau ma’ajin kwamiti sai Nasiru Fagwalawa Kano, sakataren tsare-tsare da Sabi’u Mai Manja Gamawa a matsayin mataimakin shugaba da kuma Mudassir Binanci Sokoto mataimakin sakatare.

Sannan an kafa kwamitin sasantawa da juna wanda ke karkashin shugabancin Yusif Osama Yola sai mambobin kwamitin wadana suka hada da Yasir Ramalan Gwale da Salisu H. Hafijo Katsina da Garba Tela Hadejia sai Mohammed Zakari Gombe sai Haruna Sale Kwantagora da kuma Usman Bin Affan Damaturu, inda kuma aka umarci kowane kwamiti ya ci gaba da aikin sa nan take domin samar da kyakykyawar makoma ga wannan kungiya ta muryar talaka.