Kungiyar MURIC ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta hukunta sojan da ake zargin da kashe shehin malamin nan, Goni Aisami, bayan ya roke shi ya rage masa hanya a mota.
Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan cikin wata sanrwa da ya fitar a Abuja.
- NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Tattare Da Tubar Bello Turji
- Malaman jami’o’i sun shiga wani hali —ASUU
“Tun ranar 19-8-2022 aka kashe fitaccen malamin da wani soja ya roke shi ya rage masa hanya bayan ya tashi daga aiki, a tsakiyar daji ya harbe shi sau uku har lahira.
“Baya ga haka ya tsaya kiran wani sojan dan uwansa, sakamakon motar malamin da yake kokarin guduwa da ita ta ki tashi.
“Cikin hikimar Ubangiji sai motar ta ki tashi har sai da mutane suka firfito suka ga gawar, su kuma sojojin na gefe suna kokarin tayar da motar su gudu.
“Wannan ne ya sa suka sanar da ’yan sanda, aka zo aka kama sojojin,” in ji shi.
Ya ce duk da suna yaba wa rundunar bisa wanna koakri, amma akwai bukatar ganin an dau hukunci cikin gaggawa.
“A gurfanar da su a gaban kotu kamar yadda doka ta ce, amma muna gargadin duk wanda ya yi yunkurin shirya wata manakisa kan lamarin da kakkausar murya.
“Wadannan sojoji dai sun ci amanar aikin soja, domin yayin da ’yan uwansu ke can suna hana idonsu barci don murkushe ’yan ta’adda, su fashi suke yi da kisan muatanen da ba su ja ba ba su gani ba.
Ya kuma ce sojojin da suka hada da Las Kofur John Gabriel, da Las Kofur Adamu Gideon da ke Bataliyar 241 Recce a Nguru, Jihar Yobe, sun amsa laifukansu, sai dai akwai bukatar bincikar ko da sa hannun wasu sojojin.
“Muna son sanin yadda sojan da ba ya bakin aiki ya taso tun daga Nguru zuwa Jajimaji da bindiga a hannunsa.
“Waye ya ba shi izinin daukar bindiga bayan ba ya aiki a ranar? Kuma a wane dalilin? Akwai tambayoyi da dama da muke da su suke bukatar amsa”, in ji Daraktan na MURIC.