✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muqaman hakimai ba na gado ba ne – El-Rufa’i

  Bayan rusa sababbin hakimai da dagatan da aka kirkiro a Jihar Kaduna, gwamnatin jihar ta bayyana kokarin da take yi na tantance mutum 230…

 

Bayan rusa sababbin hakimai da dagatan da aka kirkiro a Jihar Kaduna, gwamnatin jihar ta bayyana kokarin da take yi na tantance mutum 230 da suka nuna sha’awar zama hakimai a yankunan hakimai 77 na jihar.

Gwamnatin ta rusa masarautun hakimai da dagatai sama da 4000 ne ta mayar da kasashen hakiman zuwa 77 kamar yadda suke kafin zuwan gwamnatin Ahmed Makrfi wanda ya kirkiro sababbi a shekarar  2001.

Wannan mataki na gwamnatin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufa’i yana shan suka daga wadansu jama’ar jihar, sai dai Kakakin Gwamnan Samuel Aruwan ya ce masu sukar matakin gwamnatin suna yin hakan ne saboda cimma wata manufa tasu ta siyasa.

A cewarsa, gwamnati ta dauki matakin ne bayan Majalisar Zartarwar Jihar ta  amince da rahoton wani kwamiti da aka nada domin duba yadda hakimai da dagatai ke gudanar da mulkinsu a gundumominsu.

“Taron da Majalisar Zartarwa ta yi a ranar 24 ga Afrilu ya gano cewa ba a bi ka’idojin da suka kamata ba wajen kara masarautun hakimai daga 77 zuwa 390 ba lokacin wancan gwamnatin. Kuma an yi ne don cimma burin wasu a siyasance inda suka bar kananan hukumomi da tirka-tirkar yadda za su biya masarautun hakimai 313 da aka kirkiro kuma hakan ya rage kimar da hakimai da dagatai da suke da shi a idon jama’a,” inji shi.

“Yanzu dai za a tantance mutum 230 da aka karbi takardunsu na neman zama hakimai da dagatai a yankuna da gundumomin jihar. Domin a ranar 25 ga Afrilu 2017, Gwamna Nasir El-Rufa’i ya tuntubi Majalisar Sarakunan Jihar inda ya bukaci ta tattauna cikin mako biyu ta mika masa rahoto a kan lamarin.

Kuma ta ba shi rahotanta tare da nuna goyon baya ga wannan canji da ake son yi wa masarautun a cikin wata wasika da ta rubuta a ran 8 ga Mayu 2017. Wasikar ta nuna matsayar sarakunan ne a taron da suka yi a ranar  4 ga Mayun 2017. Don haka gwamnati ta yanke shawarar yin garambawul ga masarautun hakiman da dagatai. Komawa ga yankunan hakimai 77 ya nuna ke nan akwai bukatar daukar sababbin hakimai,” inji Aruwan.

Ya kara da cewa: “Gwamnati ta bukaci masarautu  32 su mika sunayen masu sha’awa domin a tantance su. Kuma ta nanata dokokin gwamnati da ke nuna cewa mukamin hakimi ba gado ba ne duk mazauna  gundumar na iya neman wannan matsayi a duk lokacin da bukatar hakan ya taso.”

Ya ce, yanzu haka masarautu 32  sun aiko da sunayen mutane da suke son a  nada su hakimai. “Sakamakon karbar sunayen, gwamnati tana binciken bayanan mutanen su 230  domin tantance su. Kuma gwamnati za ta sanar da sunayen hakimai 77 da zarar an kammala binciken tare da tantancewar,” inji shi.

Aruwan ya ce gwamnatin ta yaba wa Majalisar Sarakunan bisa kokari da ta yi wajen mika sunayen sababbin hakiman domin tantancewa.

Ya ce gwamnatin ta ki amincewa a kyale korarrun hakimai da dagatan su ci gaba da zama shugabannin al’umma a yankunansu. Domin a cewarsa, shugabannin al’umma a unguwanni ba nada su ake yi ba, jama’a ke zabar wanda suka ga ya yi musu. Ya ce wadansu daga cikin hakiman ba daga  yankunan da suke mulki suka fito ba wanda hakan ya kara nuna cewa akwai gyara sannan ba za su amince a nada su ba tare da albashi ba.

Ya ce gwamnatin tana sane da irin rikita-rikitar da ta biyo bayan rusa hakiman da dagatan, inda ya ce suna da wasiku da wadansu daga cikin hakiman da aka sauke suka musanta batun cewa sun shigar da  kara a kotu domin dakatar da wannan mataki da gwamnatin ta dauka a kansu.

“Wannan mataki an dauke shi ne da kyakyawar manufa kuma tuni masu bukata sun sake mika takardun neman zama hakimai, don haka babu bukatar surutai da wadansu ke yi,” inji shi.