Wata ’yar Najeriya kuma ’yar asalin Jihar Kano, Munayah Yusuf Hassan, ta zama kwararriyar lauya ta manyan Kotunan Ingila da Wales.
An nada ta kwararriyar lauyar manyan kotunan Birtaniya a wani kwarkwaryan biki da aka yi ranar Juma’a a Landan, a cewar fitaccen lauyan nan mai kare hakkin dan Adam, Bulama Bukarti.
- An dakatar da ’yar tseren Najeriya saboda amfani da haramtattun kwayoyi
- Matashi ya nutse a ruwa yayin ceto saniya a Jigawa
Munayah ta kammala karatunta a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan ta kammala sanin makamar aiki a Makarantar Lauyoyi kafin komawarta Ingila da mijinta.
Kwararrun lauyoyin Manyan Kotunan Ingila da Wales suna aiki da bayar da shawarwari ga abokan huldarsu akan dokokin Ingila da Wales.
Haka kuma, suna aikace-aikace da dama na shari’a a fannin dokokin kasuwanci, iyali, laifukan al’umma da sauransu.