✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna ɗaukar matakan kawo ƙarshen Lakurawa — Minista

Ministan ya ce gwamnati na buƙatar taimakon mutane wajen kawo ƙarshen 'yan ta'addan Lakurawa.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana ɗaukar matakan kawo ƙarshen sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda mai suna ‘Lakurawa’ da ke kai hare-hare a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ƙungiya ta kai hari kwanan nan, inda ta kashe mutane kuma ta sace shanu a wurare irin su Mera, Augie da ke Jihar Kebbi.

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ne, ya tabbatar da hakan cikin wata hira da aka yi da shi a BBC Hausa.

Ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙari domin daƙile Lakurawa.

“Muƙaddashin Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya ya ziyarci yankin tare da tattaunawa da sauran shugabannin soji kan yadda za a fatattaki wannan ƙungiya,” in ji shi.

“Sun tsara dabarun kawo ƙarshen ƙungiyar, ciki har da aiko da ƙarin sojoji da kayan aiki zuwa yankunan da abin ya shafa.”

Abubakar, ya ƙara da cewa shugabannin dakarun tsaro na aiki tare don hana yaɗuwar wannan tashin hankali.

“Christopher Musa, Babban Hafsan Sojin Ƙasa, tare da shugabannin sojojin ƙasa, na ruwa, da na sama sun shirya tsare-tsaren da za su magance wannan matsalar.

“Muna neman addu’arku, da taimakon Allah, za mu kawo ƙarshen wannan ƙalubalen tsaro,” in ji shi.