✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna zargin ’yan gwangwan da satar wayoyin lantarki da janaretoci a Osun – ’Yan sanda

Laifinku ya fi girma fiye da na ɓarawo domin idan babu mai sayen kayan sata ba za a samu ɓarawo ba.

Kwamishinan  ’Yan sandan Jihar Osun Mohammed Umar Abba ya zargi dillalan ’yan gwangwan da sayen wayoyin lantarki da janaretocin da ake sata daga ofisoshin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu a jihar.

Kwamishina Umar Abba ya ce a baya-bayan nan an samu ƙaruwar satar waɗannan kayayyaki a jihar.

Ya yi zargin ne a jawabin da ya yi wa shugabannin ƙungiyoyin ’yan gwangwan a wajen wani taro da su a ranar Talata a ofishinsa a Osogbo babban birnin jihar.

Kwamishinan wanda ya gayyaci dillalan don ganawa ta musamman ya ja kunnensu a kan su daina sayen kowane irin kaya da babu rasiɗi daga hannun masu sana’ar baban­bola.

Ya shaida wa dillalan cewa “Laifinku ya fi girma fiye da na ɓarawo domin idan babu mai sayen kayan sata ba za a samu ɓarawo ba.

“Kuma ci gaba da sayen kayan sata da kuke yi na ƙarfafa ayyukan sace-sace maimakon maganin haka.”

Kwamishinan wanda ya lissafo wasu wayoyin lantarki da janaretoci da aka sace daga ofisoshin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu a kwanan baya a jihar, ya roƙi ƙungiyoyin dillalan su tabbatar da haɗin kansu ga rundunar wajen hanzarta ɗaukar matakin sanar da ’yan sanda rahoton kayan da suke zargi na sata ne da aka kai masu.

Ya yi gargaɗin cewa “Idan kuka ƙi bin wannan umarni, to za mu ɗauki matakin yin dirar mikiya a dukkan ofisoshinku da wuraren da kuke ajiyar kaya.”