Rundunar ’yan sanda birnin tarayya na Abuja sun shigar da karar zargin kisa kan Maryam Sanda wacce ta kashe mijinta Bilyaminu Bello.
Mai Magana Da Yawun Rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya ce sun shigar da batun a babbar kotun tarayya mai lamba 32 da ke unguwar Jabi.
Ya ce kotun ta bayar da ummarnin garkame matar na tsawon mako biyu a gidan yari har lokacin da za a kammala bincike.