Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun ce suna tare da kwamitin rikon kwarya na shugabancin jam’iyyar karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni 100 bisa 100.
Gwamnonin sun ce hukuncin da Kotun Koli ta yanke a kwanan nan kan zaben Gwamnan Jihar Ondo shi ne ya dada karfafa musu gwiwa kan su nuna goyon bayan nasu ga shugabancin.
- Abin da ya sa zan gina jami’ar Musulunci a Daura – Rochas Okorocha
- Yadda jami’in Hukumar Kwastan ya yi sanadin mutuwar mutum 15 a Katsina
Sun dai bayyana matsayin nasu ne yayin wani taro da suka gudanar ranar Litinin don tattauna matsalolin da ke ci wa jam’iyyar tasu tuwo a kwarya.
Taron, wanda ya gudana a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi da ke unguwar Asokoro a Babban Birnin Tarayya Abuja an yi shi ne karkashin jagorancin shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu.
A cewarsu, kwamitin ya yi abin a yaba masa wajen kara karfafa jami’iyyar gabanin zaben shekara ta 2023 da ke tafe.
Taron ya kuma jaddada cewa nuna goyon bayan wata ’yar manuniya ce kan yadda suka gamsu da yadda kwalliya take biyan kudin sabulu a shugabancin.