Shugaban Kungiyar masu motocin dakon mai ta Najeriya wato NARTO, Kassim Bataiya, ya ce sun rasa mambobinsu da dama sanadiyyar hadurra da rashin tsaro a yankunan kasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne jiya Laraba a taron kungiyar karo na 18 da aka yi a Sakkwato, inda ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta inganta tsaro a yankunan Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna don dakile yin garkuwa da jama’a da ake yi.