✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna Neman Fansan Jinin Ammi Mamman —’Yar gwagwarmaya

Wata ’yar gwagwarmaya a Jihar Yobe, Laure Umaru Masokano, ta bukaci a gaggauta bincike da kuma daukar mataki kan kisan gillar wata matar aure mai…

Wata ’yar gwagwarmaya, Laure Umaru Masokano, ta bukaci gwamnati ta gaggauta bincike da kuma daukar mataki magidancin da ake zargi da yi wa matarsa kisan gillar a Jihar Yobe.

Hajiya Laure Umaru, wada ’yar siyasa ce a jihar ta ce babu dalilin da miji zai kashe matarsa, don hakan ba za su zuba ido kashe Ammi kawai, jininta ya tafi a banza ba.

Don haka tace suna son a kamo shi mijin ya yi bayanin abin da ya faru, domin rashin daukar mataki a kai zai sa wani ma ya aikata makamancin hakan.

Hajiya Laure ta bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da wakilin mu inda ta shaida cewa mijin Ammi Abubakar Musa, caka wa matar tasa wuka yayi a wuya da ya yi sanadiyar mutuwarta a lokacin da take barci ba ta san abun da ya faru ba a safiyar ranar Alhamis a rukunin gidaje na unguwar Bra-Bra a garin Damaturu.

Ta ce duk da cewa ’yan sanda sun kama wanda ake zargin, amma daukar mataki da ya dace a kansa shi ne daidai, saboda ya zama darasi ga masu irin halin.

“Me ya sa rashin Imani yake kara yawa ne a tsakanin al’umma; to wannan matarsa ma ke nan fa, ina kuma idan ba a dauki mataki a kai ba, mata nawa zai kashe’ meye tabbacin idan ya sake aure ba zai sake kashe matar ba?” In ji Laure Umaru.

Sannan tayi kira ga gwamnatin jihar Yobe da cewa ta tsaya don ganin an dauki mataki mai tsanani saboda irin wannan ta’addanci bai taba faruwa a jihar ba, idan kuma aka bari to an samu kofa ke nan.

Daga nan sai tayi kira ga Kungiyar Lauyoyi Mata da Kungiyar Amnesty International da kungiyar Human Right da sauran hukumomi da su sa ido don ganin an yi wa marigayiya Ammi adalci.