✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe dan uwan amarya, sun sace mahalarta biki a Kaduna

Cikin wadanda aka sacen har da wasu matan aure kimanin 10 da ’ya’yansu.

’Yan bindiga sun sace gomman mahalarta biki a yayin wani hari da suka kai kauyen Gidan Kunkun da ke gundumar Dawaki a Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna.

Wani jami’in tsaron sa-kai ya shaida wa Aminiya cewa an kashe mutum daya lokacin harin da aka kai ana tsaka da shagalin bikin aure.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, matashin da aka kashe mai shekaru 24 dan uwan amaryar da ake bikin auren nata ne.

Tuni dai an kai gawarsa Karamar Hukumar Ikara domin yi mata jana’iza, yayin da mutane ukun da suka jikkata — Iliyasu Ibrahim da Zaphaniya Danbala da Victor Audu — suke samun kulawa a babban asibitin garin Kauru.

Daga cikin wadanda aka tabbatar cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da su akwai Josia Sama’ila da Adamu Bulus da Enoch Bulus da Enoch Ibrahim da Yahuza Sama’ila da Lawan Francis da wani fasto a cocin Heken da ke kauyen na Gidan Kunkun da kuma wasu matan aure kimanin 10 da ’ya’yansu.

Bayanai sun ce ya zuwa yanzu dai fargaba ta lafa yayin da mutanen garin sun koma ci gaba da harkokinsu.

Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ganin cewa sun kwato mutanen da aka dauke nan ba da dadewa ba.

Kazalika, ASP Mansir ya yi kira ga al’umma da su riƙa sa ido a kan masu kai-komo a yankinsu.