✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amarya ta tura a kashe wadda mijinta zai aura ta 3

Mata ta biyu ta sa a kashe wadda mijinta zai aura ta uku

Ana neman wata matar aure kan zargin ta da sa kashe bazawarar da mijinta zai aura.

Wadda ake zargin ita ce matar magidancin ta biyu, kuma wadda mijinta yake son ya kara a matsayin ta uku, mijinta ne ya rasu.

Mai sana’ar sayar da abincin a Karamar Hukumar Ilọrin ta Yamma a Jihar Kwara ta nemi a kashe bazawarar ce da nufin hana mijinta kara aure.

Matar da ake zargin ta tsere, amma an cafke dan ina-da-kisan da ta dauka haya, bayan ya je gidan bazawarar, ya nemi ta fito domin karbar kayan tallafi.

Bazawarar mai suna Afusat ta shaida wa wakilinmu cewa, ta sha samun kiraye-kirayen barazana daga masu neman ta fasa auren.

“Da wanda ake zargin ya zo, sai ya bukaci dole sai na bi shi, shi ne na yi masa ihun barawo, makwabta suka bi shi suka kama shi a yayin da yake kokarin tserewa, suka kwace bindiga a hannunsa,” in ji ta.

Afusat ta ce “Da farko na ki amincewa da bukatar ma’aurin nawa, ​​amma daga baya na amince bayan ya dage cewa yana son in zama matarsa ​​ta uku.

“Mijina ne ya rasu, ina da ’ya’ya, ciki har da ’yan shekaru biyar da shekaru tara, kuma ni ke daukar nauyin kula da su tun da mahaifinsu ya rasu.”

Ta yi zargin cewa matar bazawarin nata ta sha yin barazanar tura mata ’yan daba idan ba ta rabu da mijina ba.

Daga nan sai ta roki jama‘a da gwamnatin jihar da su ba ta kariya tare da ya’yanta daga kisan gilla.

Kakakin yan sandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi ta tabbatar wa wakilinmu cewa “wanda ake zargin ya amsa cewa matar mutumin ce ta biya shi N10,000 ya kashe bazwarar, kuma man kama shi da bindiga; Ana ci gaba da gudanar da bincike.