Bayan shafe watanni ana kai ruwa rana kan rabuwar auren Al’Ameen G-Fresh da Sadiya Haruna, daga karshe masoyan biyu sun rabu.
Fitattun jaruman na TikTok biyu, sun shafe tsawon wata takwas ana ta kokarin yi musu sulhu amma lamarin ya cu tura.
- Matashi ya yi ninkayar kilomita 11.8 a Tekun Legas
- Mutum 4 sun mutu yayin tarwatsa ‘yan shi’a a Kaduna
A baya dai amarya, Sadiya Haruna ta maka G-Fresh a kotu, Inda ta bukaci alkali ya raba aurensu.
Sai dai ango, G-Fresh ya bayyana kotun cewar na kaunar matarsa, inda ya bukaci a kara musu lokaci domin ya samu damar yin baikon masoyiyar tasa.
A ranar 10 ga watan Oktoban 2023 ne, alkalin kotun, Abdullahi Halliru, ya bai wa ma’auratan damar yin sulhu da juna lamarin da ya yiwuwa.
Idaj ba a manta ba, an ta rade-radin cewar G-Fresh ya samu matsala da Sadiya kan wani abokinta da ta ke kira da ‘besty’ wanda a cewar wasu majiyoyi suka ce ta ƙi rabuwa da shi.
Sai dai Sadiya ta musanta wadancan zarge-zarge da ake mata.
Da ta ke bayyana yadda suka rabu a ranar Lahadi, Sadiya ta ce bai wa G-Fresh kudi Naira 500,000 inda ya amince ya rubuta mata takardar saki.
Sadiya ta bayyana wa gidan rediyon Freedom da ke Jihar Kano, cewar sun rabu yanzu kowa zai kama gabansa.
“Mun gano matsalar Malam Garba Naira 500,000 ce amma ya ƙi fada tun da farko.
“Ya bata wa shari’a lokaci saboda Naira 500,000 amma daga karshe dai ya fada kuma na ba shi.
“Ya kuma rubuta min takarda wanda hakan ke nufin aurenmu ya rabu. Ina masa fatan alheri,” a cewarta.