✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna neman afuwar Real Madrid da Liverpool —UEFA

Bai kamata a saka duk wani dan kallo cikin irin wannan hali ba.

Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar Turai UEFA, ta nemi afuwar kungiyoyin Real Madrid da Liverpool bayan magoya bayansu sun shiga halin tasku lokacin kallon wasan karshe na gasar Zakarun Turai da aka fafata a makon jiya.

Cikin sanarwar da ta fitar cikin nadama a ranar Juma’a, UEFA ta ce lamarin ba zai sake faruwa ba nan gaba.

Magoya bayan Liverpool sun bayyana cewa ’yan sanda sun kuntata musu, da haddasa yamutsi a wasan da aka buga ranar Asabar da ta gabata.

“Bai kamata a saka duk wani dan kallo cikin irin wannan hali ba kuma hakan ba za ta sake faruwa ba,” a cewar sanarwar.

Neman afuwar ya biyo bayan suka da caccaka daga magoya baya a fadin duniya game da yadda aka hana wasu da dama shiga filin wasa na Stade de France don kallon wasan duk da cewa suna da tikiti.

’Yan sandan Faransa sun ce wasu sun yi yunkurin shiga ba tare da tikiti ba, abin da ya jawo aka jinkirta soma wasan da fiye da minti 30.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta Spain ce ta lashe kofin Zakarun Turai (UCL) a karo 14 bayan doke Liverpool ta Ingila a wasan karshe da ci daya mai ban haushi a ranar Asabar ta makon jiya.

Wasan wanda ya gudana a filin wasa na Stade de France da ke birnin Paris na Faransa, inda aka samu tsaikon fara taka ledar da minti 36 sakamakon wata hananiya da ta tashi a wajen filin saboda kutsen da zargin wadansu magoya baya suka yi inda suka nemi shiga filin wasan da tikitin bogi.