’Yan sanda sun ce sun baza komarsu domin ceto kananan yara da mata da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a tsakiyar watan Ramadan a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bindiga suka yi awon gaba da kananan yara da suka je daji neman icen girki da wasu manya da suka je gona a kauyukan Wanzamai da Kucheri a karamar hukumar.
- Yadda ’yan ta’adda suka yi garkuwa da yara da mata 100 a Zamfara
- Majalisa ta amince da kudirin tilasta wa likitoci aikin shekaru 5 kafin tafiya ketare
Wani mazaunin kauyen Wanzamai, Sani Wanzamai, ya shaida wa wakilinmu cewa adadin yaran da aka yi garkuwa da su a harin na ranar Alhamis ya haura 80, manyan kuma, wadanda har da mata a cikinsu, sun kai 20.
Amma Kwamishinan ’yan sandan jihar, Yusuf Kilo, ya ce adadin bai kai haka ba, amma duk da haka suna aiki tare da sojoji da ’yan banga domin ceto mutanen da kuma mika su ga iyalansu.
A cewarsa, basaraken yankin Wanzamai ya shaida musu cewa mata tara da yara ne aka yi garkuwa da su bayan sun shiga jeji neman icen girki.
Sai dai kuma sanarwar ba ta bayyana adadin yaran da ’yan bindiga suka sace a harin na ranar 15 ga watan Ramadan, 1444 Hijiriyya ba.
Sanarwar da kakakin rundunar, CSP Mohammed Shehu, ta tabbatar cewa a yayin da masu neman icen suka nausa cikin daji ne ’yan bindiga suka bi su, suka tisa keyarsu zuwa inda ba a sani ba.