✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna kira da a zauna lafiya kan halin da ake ciki a Sakkwato  —Gwamnonin Arewa

Duk wani yunkuri na daukar doka a hannu zai iya tayar da karin rikici.

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya NGF ta yi kira da a kwantar da hankali a sakamakon tarnakin da ke neman biyo bayan kashe wata matashiya da aka zarga da yi wa Manzon Allah batanci a Jihar Sakkwato.

Cikin sanarwar da Shugaban NGF kuma Gwamnan Filato Simon Lalong ya fitar, ya ce kungiyar tasu na cikin damuwa game da halin da ake ciki a Sakkwato.

Gwamna Lalong ya yi tir da lamarin, yana mai gargadin al’umma a kan huce takaici ta hanyar daukar doka a hannunsu kan duk wani lamari da ya shafi addini ko waninsa.

“Gwamnonin sun damu da abin da ke faruwa, wanda lamari ne da ya saba wa sashen shari’a wajen daukar mataki,” a cewar Lalong.

“Gwamnonin Arewa na kiran a zauna lafiya bayan rahotannin rikidewar zanga-zangar lumana zuwa rikicin da ya sa aka saka dokar hana fita a birnin Sakkwato.”

Kazalika, gwamnonin sun ce duk wani yunkuri na daukar doka a hannu – kan lamarin addini ko akasin haka – “zai iya tayar da karin rikici”.

A yayin da NGF ke jajanta wa ’yan uwan dalibar da aka kashe, Deborah Samuel a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke birnin Shehu, ta kuma bukaci Hukumomin tsaro da su yi duk wata mai yiwuwa wajen ganin an hukunta masu hannu a lamarin.

A ranar Asabar da ta gabata ce Gwamna Nasir El-Rufai ya haramta gudanar da zanga-zangar addini a Jihar Kaduna kan batun batanci da aka yi wa Annabi Muhammadu (SAW) a Jihar Sakkwato.

Lamarin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu matasa suka gudanar ce a Sakkwato, suna masu neman jami’an tsaro su saki mutanen da suka kama bisa zargin kashe matashiyar da aka zarga da zagin Annabi.

Arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro ta jawo an harbi mutum biyu, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa manema labarai.

Rahotanni sun ce zanga-zangar ta fara ne a matsayin ta lumana kafin ta rikide zuwa jefe-jefe da duwatsu, inda su kuma jami’an tsaro suka mayar da martani da harbi da kuma hayaki mai sa hawaye.

Matasan maza da mata suna aiwatar da zanga-zangar a wurare daban-daban a fadin Sakkwato tare da kona tayoyi, da suka hada da Fadar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III.