✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi

Duk wani da ya faru a wani wuri bai kamata a ce za a ɗauki fansa a wani wurin da ba nan lamarin ya faru…

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da kashe matafiya ’yan Arewa da aka yi a Jihar Edo.

Saboda haka Sarkin ya ce suna dakon ganin hukuncin da za a ɗauka dangane da faruwar wannan mummunan lamari.

Da yake miƙa saƙon gaisuwar Sallah ga Gwamnan Sakkwato, Alhaji Ahmad Aliyu a ranar Litinin, Sarkin ya ce “mun ga an ɗauki mataki kan yanayin da ake ciki a Jihar Edo.

“Saboda haka muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka bayan kammala bincike don ba wani dalili ka kashe mutum ba tare da wani haƙƙi ba.

“Muna kiran jami’an tsaro da su tashi tsaye domin tabbatar da cewa jama’a ba su fusata ba sun ɗauki hukunci a hannunsu.

“Idan a wani wurin mutanen banza sun ɗauki hukunci a hannunsu, mu a nan Sakkwato ba za mu bari a yi abin da bai kamata ba.

“Mu sanya ’yan uwanmu da abin ya faru da su a cikin addu’a sannan muna kiran gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki matakin kare rayukkan jama’a,” a cewar Sarkin Musulmi.

Sarkin ya ƙara da cewa “bai kamata a riƙa yaɗa abin da bai dace ba a kafafen sadarwa na zamani da za su janyo tashin hankali a wurin da ake da zaman lafiya.

“Duk wani abu da ya faru a wani wuri, bai kamata wasu da ke can wani wurin na daban su ce za su ɗauki mataki a Sakkwato ko Kano ko Kaduna kan wani abun da ya faru a Jihar Edo ko Legas ba.”